Dikko Radda da wani Gwamna Sun ba EFCC Kyautar Kadarori Domin Kafa Ofisoshinta

Dikko Radda da wani Gwamna Sun ba EFCC Kyautar Kadarori Domin Kafa Ofisoshinta

  • EFCC ta mika godiyarta ga Gwamna Umaru Dikko Radda da Gwamna Biodun Oyebanji kan ba hukumar kyautar kadarori a jihohinsu
  • Shugaban EFCC, Ola Olukoyede ya ce hukumar yanzu ta samu kadarorin da za ta yi amfani da su matsayin ofishi a Katsina da Ekiti
  • Olukoyede ya bayyana hakan ne a taron da ake gudanarwa kan yaki da laifuffukan intanet da ke gudana a fadar shugaban kasa, Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnonin jihohin Katsina da Ekiti sun ba hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC kyautar wasu kadarori a jihohinsu domin kafa ofisoshinta.

Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede ne ya bayyana hakan a dakin taron fadar shugaban kasa a Abuja, inda ake gudanar da taron yaki da laifuffukan intanet.

Kara karanta wannan

Kotun Koli za ta yi hukunci kan bukatar rusa EFCC da gwamnoni 16 suka shigar

Gwamnonin Katsina, Ekiti sun ba EFCC kadarorin da za su mayar zuwa ofishi
Dikko Radda da Bidoun Oyebanji sun ba EFCC kyautar wuraren da za su kafa ofishi. Hoto: @officialEFCC, @Miqdad_Jnr
Asali: Twitter

EFCC: Taron magance laifuffukan intanet

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, an shirya taron ne tare da goyon bayan shirin kungiyar Tarayyar Turai da ke tallafa wa tsarin doka da yaki da cin hanci da rashawa (RoLAC II).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da yake maraba da manyan baki, Olukoyede ya ce hukumar EFCC ta fahimci cewa ba iya hukumar ce za a barwa alhakin yaki da aikata laifuffuka a intanet ba.

Ya ce a shekarar da ta gabata, EFCC ta hada hannu da gwamnoni, sarakuna, cibiyoyin addini, kungiyoyin matasa, kungiyoyin farar hula da dai sauransu domin a rage laifuffukan intanet.

Jihohi 2 sun yiwa EFCC kyautar kadarori

Shugaban hukumar na EFCC ya ce:

"Bari inyi amfani da wannan damar domin yabawa gwamnan jihar Katsina Umaru Dikko Radda. Ya ba mu wata kadara a jiharsa domin mu kafa ofishi.

Kara karanta wannan

Jiha 1 ta fice daga karar da aka kai EFCC, Jihohi 15 sun tsaya tsayin daka a kotu

“Amma kamar yadda kuka sani, ni dan Ekiti ce, don haka, na gaya wa gwamna cewa ina son ofishi a Jiha ta, kuma ya ba mu wurin da za mu yi amfani da shi a matsayin ofishi."

Wadanda suka halarci taron sun hada da uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu; gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya; gwamnan Zamfara, Dauda Lawal; sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar da sauransu.

EFCC ta bankado dabarun 'yan Yahoo

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar EFCC ta bayyana wasu sababbin hanyoyin damfara da masu kutsen yanar gizo ('yan yahoo) suka bullo da su.

EFCC ta ce a yanzu masu damfarar na kirkiro takardun haihuwa na bogi wurin bude asusun ajiya a bankuna domin samun daman gudanar da ayyukan damfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.