Dan damfara ya damfari hukumar EFCC a yanar gizo

Dan damfara ya damfari hukumar EFCC a yanar gizo

Wata kotun manyan laifuka ta musamman dake Ikeja a cikin birnin Legas, ta tura wani dan damfarar yanar gizo, Peter Toluwabori, gidan kaso na kirikiri a ranar Litinin dinnan sakamakon zargin shi da akeyi na lalata shaidar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa zatayi amfani da ita

An garkame wani dan damfara a kurkuku, saboda goge wata shaida da EFCC ta samu a yanar gizo
An garkame wani dan damfara a kurkuku, saboda goge wata shaida da EFCC ta samu a yanar gizo

Wata kotun manyan laifuka ta musamman dake Ikeja a cikin birnin Legas, ta tura wani dan damfarar yanar gizo, Peter Toluwabori, gidan kaso na kirikiri a ranar Litinin dinnan sakamakon zargin shi da akeyi na lalata shaidar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa zatayi amfani da ita.

DUBA WANNAN: Yanzu - yanzu: ICPC ta bada belin Darakta Janar Munir Gwarzo

Toluwabori mai shekaru 26, wanda ba a bayyana adireshin sa ba, mai shari'a Majisola Dada ya tura shi gidan kaso, bayan yace bai da laifin tuhumar shi da akeyi da laifuka biyu na lalata shaida da kuma karya dokar kasa ta hanyar aikata damfara.

"Na dage sauraron shari'ar zuwa 26 ga watan Yuni kuma wanda ake kara zai zauna a gidan kaso zuwa lokacin," cewar alkalin.

Kamar yanda Mrs Zainab Ettu, Lauyar hukumar yaki da cin hanci da rashawa tace wanda ake karar yayi laifin ne a 10 ga watan Afirilu a Ikeja, jihar Legas.

"Wanda ake zargin ya lalata wayar hannun shi, da layin MTN mai lambar waya 08100994395 da kuma layin Globacom mai lambar waya 08073175280.

"Da gangan ya lalata abubuwan don hana ayi amfani dasu gurin shaidar shari'a."

"Toluwabori ya kuma taimakawa wani Peter Samuel wanda yaje a matsayin sojan gona mai suna Daniel Johnson, ya karbi wasu codes a adireshin yanar gizo Toluwabori don aikata ta'addanci.

Laifukan sun sabawa sashi na 16(1) da 91(1) na dokar ta'addanci a jihar Legas na shekarar 2011.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng