An Yi wa Fursunoni Gata a Kano, an ba Su Kudi bayan Sakinsu

An Yi wa Fursunoni Gata a Kano, an ba Su Kudi bayan Sakinsu

  • Rahotanni sun nuna cewa ma'aikatar shari'a ta jihar Kano ta yi afuwa ga wasu yan fursuna domin rage cinkoso a gidajen gyaran hali
  • Alkalin alkalan jihar, mai shari'a Dije Abdu Aboki ta fitar da yan kurkukun ne daga gidan gyaran hali na Goron Dutse da ke birnin Kano
  • Mai shari'a Dije Abdu Aboki ta yi kira na musamman ga yan kurkukun da aka yi wa afuwar tare da yi masu kyautar kuɗi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Bayan sakin fursunoni a jihar Zamfara, ma'aikatar shari'a a Kano ta yi afuwa ga yan kurkuku 37.

Alkallin alkalan jihar, mai shari'a Dije Abdu Aboki ce ta yi afuwa ga yan fursunan tare da faɗin dalilin sakinsu.

Kara karanta wannan

Bobrisky: Asirin shahararren Ɗan daudu ya tonu yana shirin tserewa a iyakar Najeriya

An saki
An saki yan fursuna a Kano. Hoto: kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa mai shari'a Dije Abdu Aboki ta yi wa fursunonin kyautar kuɗi domin hawa mota zuwa gida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi afuwa ga fursunoni a Kano

Jaridar Punch ta wallafa cewa alkallin alkalan jihar Kano, mai shari'a Dije Abdu Aboki ta yi afuwa ga wasu yan fursuna guda 37.

Mai shari'a Dije Abdu Aboki ta yi nasiha ga wadanda aka yi wa afuwar da su nisanci aikata laifin da zai iya dawo da su gidan yarin a gaba.

Dalilin sakin yan fursuna a jihar Kano

Mai shari'a Dije ta bayyana cewa wasu daga cikin yan fursunan ba su da lafiya kuma an sake su ne domin su je neman magani.

Ta kuma kara da cewa wasu yan fursunan sun dade a kulle ba tare da mika su gaban alkali ba har takardunsu suka bata.

Kara karanta wannan

'Ku yi masu addu'a kawai': Uwargidan Tinubu ta gargadi malamai kan zagin masu mulki

An yi wa yan fursuna kyautar kuɗi a Kano

Biyo bayan sakin yan kurkukun, ma'aikatar shari'a ta musu kyautar N10,000 domin samun kudin acaba.

Shugaban gidan kurkukun Kano, Ado Inuwa ya mika godiya ga ma'aikatar shari'a kan halin girma da ta nuna wajen yin afuwa ga yan kurkukun.

An sake yan fursuna a jihar Zamfara

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta yi afuwa ga wasu yan kurkuku domin rage cinkoso.

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa dole a rika mayar da hankali ga gidajen gyaran hali bisa lura da yan bindiga da ake yawan kamawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng