Yanzu-yanzu: Buhari ya bada umurnin sakin fursuna 2,600

Yanzu-yanzu: Buhari ya bada umurnin sakin fursuna 2,600

Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin sakin yan gidan yari 2,600 a fadin tarayya domin rage cinkoso cikin gidajen gyara halin Najeriya.

Shugaban kasan ya bi sahun sauran shugabannin kasashen duniya wajen yafewa fursunonin domin rage yawansu a gidajen yari saboda cutar Coronavirus.

Hadimin shugaba Buhari kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad, ya ruwaito Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, da fadin hakan a ranar Alhamis, 9 ga watan Afrilu, 2020 a hira da yayi da manema labarai.

Yace: “Shugaba Muhammadu Buhari ya yafewa fursunoni 2,600 a fadin tarayya cikin yunkurin rage izdihami a gidajen gyara halin domin takaita yaduwar cutar Coronavirus.“

A cewarsa, za a saki fursuna 70 daga gidan yarin Kuje da ke Abuja a yau Alhamis, sannan daga baya a saki fursunonin dake gidajen yarin sauran jihohi irinsu Kiri-kiri Dss.

Yanzu-yanzu: Buhari ya bada umurnin sakin fursuna 2,600
Yanzu-yanzu: Buhari ya bada umurnin sakin fursuna 2,600
Asali: Twitter

Ga jerin fursunonin da aka yafewa

1. Tsofaffi masu shekaru akalla 60

2. Masu fama da rashin lafiya mai tsanani

3. Fursunonin da wa'adinsu da ya rage na kasa da watanni shida

4. Masu ciwon tabin hankali

5 Wadanda aka ci tarar su kasa da N50,000.

Amma ya bayyana cewa ba za a saki wadanda aka kama da laifin ta'addanci, satar mutane da kisan kai ba.

A bangare guda, Hukumar yaki da hana yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC), ta karyata rahotannin da ke ikirarin cewa ta kashe kimanin naira biliyan daya wajen aike wa yan Najeriya sakonnin waya kan yadda za su kauce wa kamuwa da cutar coronavirus.

A wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, hukumar ta NCDC ta jadadda cewa ko da yake sadarwa na cikin manyan hanyoyin yaki da annobar covid-19, amma kamfanonin wayar salula ne suka dauki nauyin aike wa da irin wadannan sakonni a matsayin nasu gudunmawar.

Ya zuwa daren ranar Laraba, 8 ga watan Afrilu dai, NCDC ta ce mutane 276 ne suka kamu da coronavirus a kasar, yayin da aka sallami mutane 44 bayan sun warke, mutane shida sun mutu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng