Jiha 1 Ta Fice daga Karar da Aka Kai EFCC, Jihohi 15 Sun Tsaya Tsayin Daka a Kotu

Jiha 1 Ta Fice daga Karar da Aka Kai EFCC, Jihohi 15 Sun Tsaya Tsayin Daka a Kotu

  • A yau ake zama kan shari'ar jihohi 16 a Najeriya da hukumar yaki da cin hanci ta EFCC a birnin Tarayya Abuja
  • Jihohin 16 sun shigar da korafi ne inda suke kalubalantar dokar da ta samar da hukumar da cewa an kafa ta babu ka'ida
  • Tun farko jihar Kogi ce ta fara shigar da korafi kan dokar kafin daga bisani jihohi 15 su mara mata baya kan shari'ar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Yayin da ake cigaba da zama kan korafi da aka shigar da EFCC, jihar Anambra ta janye daga shari'ar.

Jihar ta janye korafin na ta bakin kwamishinan shari'a a Anambra, Farfesa Sylvia Ifemeje a yau Talata 22 ga watan Oktoban 1 2024.

Kara karanta wannan

Kotun Koli za ta yi hukunci kan bukatar rusa EFCC da gwamnoni 16 suka shigar

Jiha 1 ta ware kanta a shari'ar da ake yi kan hukumar EFCC
Jihar Anambra ta janye korafinta game da kalubalantar ƙirƙirar hukumar EFCC. Hoto: Charles Soludo, Economic and Financial Crimes Commission.
Asali: Facebook

Anambra ta janye daga korafi kan EFCC

Jaridar Vanguard ta ce ana cigaba da sauraran shari'ar korafi kan dokar da ta kirkiri hukumar EFCC a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun farko, gwamnatin jihar Kogi ce ta fara shigar da korafin kan hukumar EFCC game da dokar da ta samar da ita.

Daga bisani jihohi 15 suka mara mata baya game da kalubalantar dokar da ta samar da EFCC.

Wanda ke kare hukumar EFCC a shari'ar

Ministan shari'a, Lateef Fagbemi ya kasance mutum daya da yake kare dokar da ta kirkiri hukumar EFCC.

Yayin da jihar Anambra ta sanar da ficewarta a shari'ar, Fagbemi bai kalubalanci matakin nata ba, Channels TV ta ruwaito hakan.

Farfesa Sylvia Ifemeje yayin ficewa daga shari'ar ya ce jihar ba ta da sha'awar cigaba da kasancewa a korafin da jihar Kogi ya soma.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Abuja, 'yan ta'adda sun kashe babban jami'in gwamnati

EFCC ta kwato N200bn a shekara 1

Kun ji cewa Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta samu nasarar ƙwato maƙudan kuɗi a hannun ɓarayi.

EFCC ta ƙwato sama da N200bn a shekara ɗaya a ƙarƙashin jagorancin Ola Olukoyede wanda ya fara aiki a Oktoban 2023.

Kakakin hukumar EFCC da ya bayyana hakan ya ce an kuma yanke hukunci ga mutane 3000 waɗanda aka samu da laifi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.