Gyaran Tattalin Arziki: Manyan Nasarori 5 da Gwamnatin Tinubu Ta Samu a 2024
Abuja - Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa ana samun gagarumar nasara a gyaran tattalin arziki da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu take yi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
A cewar fadar shugaban kasar, sai 'yan Najeriya sun jurewa duk wani tsanani da za a fuskanta a yanzu domin samun ci gaba mai dorewa a nan gaba.
Mai ba da shawara na musamman ga Shugaba Tinubu kan tsare-tsare da watsa labarai, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.
A cikin sakon da ya wallafa, Onanuga ya lissafa wasu manyan nasarori biyar da gwamnatin Tinubu ta samu kan tattalin arziki a shekarar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nasarorin gwamnatin Tinubu kan tattalin arziki
1. Nasara a samun rarar ciniki
A watanni uku na farkon shekarar 2024, Najeriya ta samu rarar ciniki na Naira tiriliyan 6.527. A zango na biyu na shekarar, rarar ta karu zuwa tiriliyan 6.944.
A lokacin da shekarar 2024 ta je tsakiya, Najeriya ta samu kudin cinikayya da kai rabin kudin kasafin kasar na tiriliyan 28.77.
Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta ce kudin da kasar ta samu a fitar da kaya ya kai Naira tiriliyan 19.4 yayin da ta samu Naira tiriliyan 12.4 a shigo da kaya.
Cinikin danyen mai a cewar rahoton NBS shi ne ya mamaye kasuwancin Najeriya a bangaren fitar da kaya waje a zango na biyu na 2024, inji The Nation.
A cikin zango na biyu na 2024, kasar Sin ta kasance babbar abokiyar cinikayyar Najeriya a bangaren shigo da kayayyaki, sai Belgium Indiya, Amurka da kuma Netherlands.
2. Nasarar daina shigo da mai
A karon farko cikin shekaru 40, Najeriya ta kawo karshen shigo da mai daga ƙasashen waje. Sakamakon fara aikin matatar Dangote, yanzu kasar na fitar da fetur, gas zuwa waje.
Rahoton Arise News ya nuna cewa daga ranar 1 ga watan Oktoba, NNPC ya fara samar da danyen mai na kusan ganga 385,000 a kowace rana ga matatar Dangote.
Kamfanin man Najeriya (NNPC) ya daina sanya bukatun shigo da mai cikin kasar daga Oktoba, wanda ya zama gagarumar nasara a tsayawar Najeriya da kafafunta.
Jaridar Punch ta rahoto shugaban NNPCL, Mele Kyari ya ce Najeriya za ta zama babbar mai fitar da mai da iskar gas a watan Disambar shekarar nan.
Alkaluma daga fannin makamashi da iskar gas sun nuna cewa idan matatun Fatakwal, Kaduna da Warri suka kama aiki, to kasar za ta ciri tuta a fitar da mai.
3. Asusun kudin kasar waje
Kudaden ajiyar Najeriya a kasar waje ya kai dala biliyan 39.07 a Satumbar 2024, wanda ya sa kasar ta magance rikice-rikicen tattali da aka taba ganin ya faru a Venezuela da Zimbabwe.
An samu wannan gagarumar nasarar ne sakamakon matakan da bankin CBN ya dauka na ba da fifiko a tara kudaden ajiyar maimakon daidaita kudin wucin gadi na AC.
Da yake zantawa da This Day, ministan kasafin kudi da tsare-tsare tattalin arziki, Abubakar Atiku Bagudu, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya samu nasarar shawo kan matsalar tattalin arziki.
Bagudu ya ce aiwatar da tsare-tsaren mulki da yiwa hukumomi garambawul ya taimaka wajen inganta ayyukan tattalin arziki a Najeriya.
"Kudin ajiyarmu na kasar waje ya kai dala biliyan 39.07 ya zuwa 19 ga Satumbar 2024. Kudin kasuwancinmu na waje ya karu zuwa Naira biliyan 6,945.4 a zango na biyu na 2024."
- A cewar ministan.
4. Cigaban karfin tattalin arziki a 2024
Tattalin arzikin Najeriya ya habaka da kaso 3.19% a cikin watannin Afrilu zuwa Yunin 2024 idan aka kwatanta da kimar tattalin a 2023.
Rahoton Reuters ya nuna cewa tattalin arzikin Najeriya ya samu karuwa da kashi 2.51 a 2023 amma ya kai kashi 3.19 a 2024 wanda ya zarce kashi 2.88 na tsakanin Janairu zuwa Maris.
Wanann kuwa ya biyo bayan bunkasar fannin mai da gas da aka samu na kaso 10.15 da kuma bunkasar noma da kaso 1.41 tare da bunkasar kaso 3.53 a fannin masana'antu.
Najeriya ta sami karuwar man fetur na yau da kullum, inda ta ke iya fitar da ganga miliyan 1.41 a kowace rana a zango na biyu na 2024, sama da gangan miliyan 1.22 da take fitarwa a 2023.
Tun da fari, asusun ba da lamuni na duniya (IMF) ya yi hasashen tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa da kashi 3.1 a shekarar 2024, kuma zuwa yanzu an ga faruwar hakan.
5. Cigaba a hada-hadar kasuwar jari
Kasuwar hada hadar hannayen jari ta Najeriya ta kafa tarihi sau hudu a cikin watanni 16. Ranar 1 ga Nuwamba, 2023, hannun jarin NGX ya kai kololuwar darajarsa da karin kaso 1.9% a cikin kwana ɗaya (70,581.76).
A ranar 10 ga Janairu, 2024, hannun jarin NGX ya samu kudin da suka kai tiriliyan 1.6 kuma darajar hada hadarsa ta kai 83,191.84 (ASI).
A ranar 24 ga Janairu, 2024 kuwa, NGX ya tsallake darajar hada hada ta 100,000, inda ya zama hannun jari mafi riba a kasuwar duniya.
Hakazalika, ranar 28 ga Maris, 2024, darajar hada hadar NGX ta kai 104,562.06, wanda ya kai karin kaso 39.84 idan aka kwatanta da 2023, kuma ya zamo hannun jari na biyu mafi daraja a Afrika.
'Dalilin samar da manufofin tattali' - Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaba Bola Tinubu ya rarrashi 'yan Najeriya kan wahalhalun da suke fuskanta sakamakon manufofin tattalin arziki da ya kawo.
A wani taron akantoci na kasa, karo na 54 da ya gudana a Abuja, Tinubu ya jaddada cewa manufofin da ya kawo sun taimaka wajen hana Najeriya fadawa mawuyacin hali.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng