Yadda Kwankwaso, Peter Obi, Abba da Jiga Jigan NNPP Suka Hadu yayin Tarbar Dalibai

Yadda Kwankwaso, Peter Obi, Abba da Jiga Jigan NNPP Suka Hadu yayin Tarbar Dalibai

  • A yammacin ranar Litinin gwamnatin Kano ta shirya tarbar daliban da Abba Kabir Yusuf ya tura karatun digiri na biyu zuwa kasar Indiya
  • Tawaga ta musamman da ta haɗa da madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ta karbi daliban bayan isowarsu birnin Kano
  • A yayin tarbar daliban, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya hadu da dan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi a filin jirgin sama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamnatin Kano ta shirya tarba ta musamman domin karbar daliban jihar da aka tura karatu kasar Indiya.

An ruwaito cewa manyan jami'an gwamantin Kano ne suka tarbi daliban a filin jirgin saman Malam Aminu Kano.

Kara karanta wannan

Ana raɗe raɗin wargajewa, gwamna Abba ya tura saƙo ga Kwankwaso

Kwankwaso
Gwamnatin Kano ta tarbi dalibai da suka dawo daga Indiya. Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Hadimin Sanata Kwankwaso, Saifullahi Hassan ne ya wallafa bidiyon yadda lamarin ya faru a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso, Peter Obi da Abba sun hadu

Yayin tarbar daliban jihar Kano da aka tura karatu, Sanata Kwankwaso, Abba Kabir Yusuf da manyan yan NNPP sun hadu da Peter Obi.

An hango Peter Obi da Kwankwaso suna magana suna dariya bayan gaisuwa da suka yi a filin jirgin saman Malam Aminu Kano.

Cikin tawagar Peter Obi akwai hadiminsa, Yunusa Tanko haka zalika Kwankwaso yana tare da Isaac Idahosa.

Daliban Kano da aka tarba daga Indiya

Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta tarbi dalibai 29 da suka dawo daga Indiya.

Rahotanni na nuni da cewa dukkan daliban su 29 sun kammala karatun digiri na biyu a jami'ar SR ta kasar Indiya.

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya nada kawun Gwamna Abba Kabir Yusuf babban matsayi a masarautar Kano

Gwamna Abba ya yi wa daliban Kano alkawari

Bayan karɓar daliban, gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin ba dukkansu aiki a ma'aikatun gwamnatin jihar Kano.

Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa zai ba daliban aiki ne domin kawo cigaba a jihar Kano bayan sun samo ilimi mai zurfi a duniya.

Abba ya taya Kwankwaso murna

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya taya Rabi'u Musa Kwankwaso murnar cika shekaru 68 da haihuwa.

Gwamna Abba Kabir ya bayyana cewa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso gwarzo ne a siyasar kasar nan kuma ya bayar da gudummawa sosai wajen cigaban Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng