Hukumar FIRS Za Ta Dauki Ma’aikata, Ta Bayyana Wadanda Suka Cancanci Neman Aikin
- Hukumar tara kudin shiga ta tarayya (FIRS) ta aika sako ga 'yan Najeriya da ke son yin aikin gwamnati a matsayin jami'an haraji
- FIRS ta bayyana cewa za ta dauki ma'aikata a bangaren jami'an haraji na daya da na biyu kuma tana neman masu sha'awar aikin
- Hukumar ta nemi wadanda ke son bajintarsu a aikin gwamnati da bayar da gudummawa ga ci gaban kasa da su nemi aikin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A yayin da matasan Najeriya ke korafin rashin ayyukan yi, hukumar tara kudin shiga ta tarayya (FIRS) ta sanar da fara daukar ma'aikata.
Hukumar FIRS ta bayyana cewa tane neman matasan da suka kammala karatun gaba da sakandare domin su nemi aikin jami'an haraji a hukumarta.
Hukumar FIRS za ta dauki ma'aikata
Hukumar ta sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X (tsohon Twitter) a ranar Litinin, 21 ga Oktoba, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce hukumar za ta dauki ma'aikata a matakin jami'in haraji na daya da na biyu.
A cikin sanarwar, FIRS ta bayyana cewa nan gaba kadan za ta fitar da cikakkun bayanai game da tsarin neman guraben aikin.
Za a ji lokacin fara nema da gamawa da sauran bayanai a shafinta na intanet.
“Hukumar tara kudin shiga ta tarayya (FIRS) hukuma ce da ke ba kowanne dan Najeriya da ya cancanta damar yin aiki da ita."
- Inji sanarwar.
"Wadanda suka cancanta su nema" - FIRS
Sanarwar ta bayyana cewa:
"Muna bukatar matasan da suke da daraja da kuma burin samun ci gaba a aiki, sannan muna neman wadanda suke da basira a kididdiga, warware matsaloli da kwarewa a sadarwa.
"Muna ƙarfafa guiwar duk wadanda suka san sun cancanta da su nemi aikin ba tare da la'akari da jinsi, kabila, ko asalinsu ba.
"Ku kasance tare damu domin samun ƙarin bayanai, kuma muna godiya da kuka nuna sha'awarku ta yin aiki tare da hukumar FIRS."
Gwamna zai dauki ma'aikata 17,000
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan Kano, Abba Kabiru Yusuf ya sanar da shirinsa na daukar sababbin ma'aikata har 17,000 a fadin jihar.
Gwamnatin Kano za ta ɗauki jami'ai mafarauta aikin tsaro a wani ɓangare na kokarin bunƙasa harkokin ilimi da ke fuskantar barazanar tsaro.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng