Akwai yiwuwar albashin ma’aikatan Hukumar FIRS ya ragu a dalilin rikicin VAT da Gwamnoni

Akwai yiwuwar albashin ma’aikatan Hukumar FIRS ya ragu a dalilin rikicin VAT da Gwamnoni

  • Hankalin ma’aikatan FIRS ya tashi saboda yunkurin hana su karbar VAT
  • Idan jami’an FIRS suka daina karbar VAT, kudin shiga zai ragu sosai a 2023
  • Ana tsoron za a rage wa ma’aikatan albashi idan abin da ake samu ya ragu

Jaridar Punch tace an samu karin wasu jihohi biyu bayan Legas da Ribas da za su kawo dokar da za ta ba su damar karbar harajin VAT da kansu.

Akwa Ibom da Ogun za su shiga sahun gwamnatocin Ribas da kuma Legas da za su hana jami’an FIRS tattara harajin kayan masarufi a Jihohinsu.

Rahoton yace a daidai wannan lokaci ma’aikatan hukumar FIRS da ke karbar VAT sun tsure a game da wannan mataki da gwamnoni ke dauka.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Kotun daukaka kara ta hana jihar Legas da Rivers karbar kudin harajin VAT

Wasu malaman haraji sun shaida wa jaridar cewa karbe ikon tattara haraji daga hannun FIRS a jihohi zai rage kudin-shigar da hukumar ke samu.

Za a rasa N96bn a duk shekara

Idan aka hana ma’aikatan FIRS karbar haraji a jihohi, abin da suke tatsa a shekara zai ragu da N96bn.

Hukumar ta bayyana wa majalisar tarayya cewa tana harin N2.44tr daga harajin kayan masarufi a 2022, daga ciki ne FIRS zai dauki 4% na kason VAT.

Hukumar FIRS
Ofishin FIRS Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Inda FIRS take samun kudin-shiga sune da harajin fetur, VAT, harajin hatimi da na kamfanoni. VAT na cikin hanyar da FIRS ta fi samun kudin-shiga.

“Idan muka daina karbar harajin VAT, hukumar FIRS ba za ta iya biyan alawus da sauran kudi na musamman da ake ba ma’aikata ba.”

Kara karanta wannan

Dokar VAT za ta talauta Jihohi 30, Gwamna Wike yace sai dai sama da kasa su hade

“A halin yanzu hankalinmu ya tashi, domin bamu san abin da zai faru a nan gaba ba.”

Wani babban ma’aikacin hukumar ya bayyana cewa FIRS ta dauki ma’aikata barkatai don haka dole a rage yawan ma’aikata idan aka daina karbar VAT.

Nyesom Wike ya kafe

Duk da kun ji cewa dokar VAT za ta talauta Jihohi 30 a Najeriya, Gwamnan Ribas, Nyesom Wike yace sai dai sama da kasa su hade, ba zai janye kara a kotu ba.

Gwamnoni 30 ba za su iya rike kansu ba idan aka kyale jihohi da alhakin VAT. Gwamnan jihar Ribas yace babu ja da baya a shari'arsa da gwamnain tarayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel