Yan Sanda Sun Cafke Dattijuwa da Harsasai 350 Za Ta Kai wa Ƴan Bindiga
- 'Yan sandan Yobe sun kama wata mata mai suna Hamsatu Modu ‘yar shekara 54 a kauyen Morami da ke Konduga a jihar Borno
- Jami'ai sun kama Hamsat da laifin safarar alburusai 350 daga garin Buni Yadi da ke Borno zuwa Damaturu, babban birnin Yobe
- Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Yobe, Dungus Abdulkarim ya bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne a ranar Lahadi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Yobe - Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta ce ta kama wata Hamsatu Modu mai shekaru 54 dauke da harsasan bindiga 350.
An rahoto cewa 'yan sanda sun cafke dattijuwar ne a kauyen Morami da ke karamar hukumar Jakana Konduga ta jihar Borno.
An cafke dattijuwa da harsasai
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Dungus Abdulkarim, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce ana zargin Hamsatu Modu ta dauko alburusan ne daga garin Buni Yadi domin kaiwa 'yan bindiga a Yobe.
DSP Dungus ta kara da cewa jami’an ‘yan sanda na ‘A’ reshen ofishin rundunar da ke Damaturu, babban birnin jihar ne suka kama wanda ake zargin.
Channels TV ta rahoto jami'in hulda da jama'ar ya ce:
“A wani bincike da aka yi cikin wata motar kirar Golf 3, jami'an sun gano harsasai masu tsayin 7.62 × 39 MM guda 350 da aka boye a cikin kayan wadda ake zargin."
'Yan sanda na bincikar dattijuwar
A cewarsa, rundunar ‘yan sandan ta samu sahihan bayanan sirri cewa wata da ake zargin tana safarar makamai ga 'yan bindiga ta na kan hanyar zuwa Damaturu.
Wannan ne dalilin tsaurara matakai tare da kafa shingayen bincike, lamarin da ya kai ga nasarar cafke wanda ake zargin dauke da harsasan.
"A halin yanzu wanda ake zargin ta na fuskantar tambayoyi yayin da masu bincike ke aiki domin bankado wadanda ke daukar nauyinta da kuma makasudin safarar harsasan."
- A cewar DSP Dungus.
An cafke mai safarar makamai
A wani labarin, mun ruwaito cewa jami’an tsaro sun cafke wata Aisha Abubakar dauke da alburusai da ake zargin za ta kai wa 'yan ta'adda a jihar Katsina.
Tun da farko matar ta ki amsa cewa harsasan na ta ne a lokacin da aka gansu cikin kunshin kayanta amma bayan tsaurara bincike ta amsa cewa ita ce mai su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng