Obasanjo Ya Fadi Kokarin da Ya yi da Yake Mulki, Ya Koka da Rashin Tsaro a Yau

Obasanjo Ya Fadi Kokarin da Ya yi da Yake Mulki, Ya Koka da Rashin Tsaro a Yau

  • Tsohon shugaban kasar nan, Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa akwai babban kalubalen karuwar rashin tsaro a Najeriya
  • Ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci jihar Bauchi a wani bangare na kaddamar da ayyukan gwamnatin Bala Mohammed
  • Cif Olusegun Obasanjo ya shawarci gwamnatin Najeriya ta yi abin da gwamnatinsa ta yi na mutunta rayuka da dukiyoyin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Bauchi - Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya yi takaicin karuwar rashin tsaro da ke kamari a fadin kasar nan.

Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana takaicinsa a lokacin da ya ziyarci fadar Mai Martaba Sarkin Bauchi, Rilwanu Suleiman-Adamu a fadarsa.

Kara karanta wannan

'Ta dawo makabarta': Obasanjo ya fadi dalilin rashin samun cigaba a Najeriya

Obasanjo
Obasanjo ya shawarci gwamnati kan rashin tsaro Hoto: Senator Bala AbdulKadir Mohammed
Asali: Facebook

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa tsohon shugaban kasar a mulkin soja da farar hula ya ziyarci Bauchi ne domin kaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin jihar ta samar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Olusegun Obasanjo ya fadi ayyukan gwamnatinsa

Jaridar Punch ta tattaro Cif Obasanjo na cewa gwamnati ta mutunta tsaron rayukar yan Najeriya a lokacin da ya ke shugabantar kasar.

Ya bayyana cewa lamarin tsaro a kasar nan ya tabarbare matuka, har ya jaddada bukatar da ake da ita na gwamnati ta dauki matakan tsare rayukan jama'a.

Shugaba Obasanjo ya bayar da shawara kan tsaro

Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya shawarci jama'a da su san makotansu, domin wannan na daga hanyar tabbatar da tsaro.

Ya ce idan mutane sun san wadanda su ke makotaka da su, za a gaggauta gano baragurbin cikin al'umma tare da mika su ga jami'an tsaro.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya caccaki yadda Tinubu, Shettima su ka bar Najeriya da matsala

Obasanjo ya fadi babbar barzanar tsaro

A baya mun ruwaito cewa tsohon shugaban kasar nan, Cif Olusegun Obasanjo ya ce yawaitar yara marasa zuwa makaranta za su zama babbar barazana ga tabbatar da tsaron kasar nan.

Tsohon shugaban ya ce yaran da ba sa zuwa makaranta za su iya zama wadanda yan Boko Haram ko sauran marasa gaskiya ke dauka domin cigaba da ayyukan rashin tsaro a sassa daban-daban.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.