'Zai Gaji Mahaifinsa': Gwamna Abba Ya Mika Sandar Mulki ga Sarkin Gaya Aliyu

'Zai Gaji Mahaifinsa': Gwamna Abba Ya Mika Sandar Mulki ga Sarkin Gaya Aliyu

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya mika sandar mulki ga Mai Martaba Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim a ranar Lahadi
  • Gwamnan na Kano ya bukaci sarkin da ya kasance abin koyi ga al'ummarsa tare da yin shugabanci bisa tafarkin addinin musulunci
  • An rahoto cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II na daga cikin wadanda suka halarci taron mika sandar mulkin ga Sarki Aliyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Gaya, Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya mika sandar mulki ga sabon sarkin masarautar gaya da aka nada, Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir.

Bayan rushe masarautun Kano a 2024, Gwamna Abba ya amincewa Sarki Aliyu ya ci gaba da zama kan kujerar mahaifinsa, marigayi Ibrahim Abdulkadir.

Kara karanta wannan

Musulmai sun magantu kan zargin shirin rushe masallacin Juma'a, sun ba gwamna shawara

Gwamna ya yabi Sarkin Gaya yayin da ya ke mika masa sandar mulki
Gwamnan Kano, Abba Yusuf ya mika sandar mulki ga sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

An mikawa sarkin Gaya sandar mulki

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a daren ranar Lahadi, 20 ga Oktobar 2024, Gwamna Abba ya ce Sarki Aliyu "mutumin kirki ne."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II na daga cikin manyan bakin da suka halarci taron mika sandar girman ga sabon sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim.

Gwamna Abba ya ce:

"Na yi farin cikin gabatar da sandar mulki ga Mai Martaba Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir, yau (Lahadi) a Gaya."

'Sarkin Gaya mutumin kirki ne' - Abba

Gwamnan jihar Kano ya bayyana Sarki Aliyu Ibrahim a matsayin mutum mai gaskiya, saukin kai da kuma dattako yana mai cewa:

"Ina da yakinin cewa zai kasance mai rikon amana da zamowa shugaba abin kwatance yayin ci gaba da jagorantar mutanen masarautarsa."

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya nada kawun Gwamna Abba Kabir Yusuf babban matsayi a masarautar Kano

Mai girma Abba ya kuma ce yana da yakinin cewa sarkin zai gaji kyawawan dabi'u na mahaifinsa, marigayi Sarki Ibrahim Abdulkadir ta hanyar yin shugabanci bisa turbar Islama.

Gwamna ya dawo da sarkin Gaya

Tun da fari, mun ruwaito cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake dawowa da Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir a matsayin sarkin masarautar Gaya.

An ce gwamnan ya mayar da Sarki Aliyu kan kujerarsa ne sakamakon biyayyar da ya nuna ga hukuncin da gwamnati ta dauka na rusa masarautun Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.