Ganduje ya mika takardar kama aiki ga sabon Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya

Ganduje ya mika takardar kama aiki ga sabon Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya

  • Gwamnan Kano ya rantsar da sabn Sarkin Gaya kwana daya bayan alantasa
  • Ganduje ya mika masa takardan kama aiki gadan-gadan
  • Sabon Sarkin ya mika gpdiyarsa ga gwamna Ganduje

Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya jagoranci rantsarwa tare da mika takardar kama aiki ga sabon Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya Wanda aka gudanar a dakin taro na Coronation dake Gidan Gwamnati.

Gwamna Ganduje ya hori sabon Sarkin da ya jajirce a bangaren aikin yan sanda da al’umma a yankin sa domin tallafawa kokarin Gwamnati na samar da tsaro a wannan masaurauta.

Gwamnan ya kuma kara tabbatar da kudirin Gwamnatin sa na cigaba da kara samar da tituna a sabbin masarautu hudu tare da daga darajar asibitocin su zuwa masu cin gadaje dari hudu duk a yunkurin da Gwamnatin sa na mai da su Kananan birane.

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Gwamnan ya kuma yi amfani da damar wajen yiwa daukacin al’ummar masarautar Gaya ta’aziyyar rasuwar Marigayi Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim Abdulqadir wanda ya rasu ranar Larabar da ta gabata.

Ganduje ya mika takardar kama aiki ga sabon Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya
Ganduje ya ika takardar kama aiki ga sabon Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya Hoto: Aminu Dahiru SSA Photography
Asali: Facebook

Sabon Sarki yayi godiya ga Gwamna

A jawabin sa na godiya Mai Martaba Sarkin Gaya ya godewa Allah sannan ya godewa mai Girma Gwamna da kuma masu nada sarki da al'ummar Masarautar Gaya bisa yarda dashi a matsayin Sarkin su.

Sarkin ya kuma tabbatar da cewa zaiyi aiki tukuru musamman a bangare ilimi da kiwon lafiya ya kuma yabawa yan uwan sa da kuma kira akan su hada kai domin ciyar da masauratar gaba.

Su wa suka halarci taron rantsarwan?

Taron ya samu halartar sarakunan Kano masu daraja ta daya wato Mai Martaba Sarkin Karaye da Mai Martaba Sarkin Rano da wakilan Masu Martaba Sarakunan Kano dana Bichi da hakimai da sauran yan majalisun su.

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Yakasai ya lissafa 'yan siyasa 3 na kudu da ka iya nasara a matsayin dan takarar APC

Gwamnan yana tare da sakataren Gwamnati, Alhaji Usman Alhaji da shugaban Jamiyyar APC, Alhaji Abdullahi Abbas da dattijo Alhaji Nasiru Aliko Koki da kwamishinan Kananan hukumomi da harkokin masautu Hon. Murtala Sule Garo da yan majalisun jiha dana tarayya da kwamishinoni da chiyayamomin Kananan hukumomi da sauran jami'an Gwamnati.

Mun kawo muku cewa Gwamna ya amince da nadin Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya a matsayin sabon sarkin masarautar Gaya.

Wannan ya biyo bayan zabinsa da masu zaben Sarkin masarautar sukayi.

Sakataren Gwamnatin jihar, Usman Alhaji, ya bayar da wannan sanarwa a gidan gwamnatin jihar yayinda aka karbi bakuncin masu zaben Sarki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel