"Ba Laifin Tinubu ba ne:" Akpabio Ya Gano Yadda Tattalin Arziki Ya Samu Matsala

"Ba Laifin Tinubu ba ne:" Akpabio Ya Gano Yadda Tattalin Arziki Ya Samu Matsala

  • Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na kokarinta
  • Ya ce lalacewar tattalin arzikin Najeriya ta samo asali ne daga gwamnatocin baya, ba a wannan gwamnatin da ke mulki ba
  • Sanata Godswill Akpabio ya jaddada cewa za a ji dadin matakan da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke samarwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja Shugaban majalisar dattawa, Godswill Apkabio ya tabbatarwa yan kasar nan cewa ba a gwamnatin Bola Tinubu aka samu matsalar tattalin arziki ba.

Sanata Godswill Apkabio ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, inda ya jaddada cewa tattalin arzikin kasar nan ya samo asali ne daga gwamnatocin baya.

Kara karanta wannan

‘Yan APC da suka koma kuka da gwamnati saboda tsadar rayuwa a zamanin Tinubu

Tinubu
Akpabio ya dora laifin lalacewar tattalin arziki kan gwamnatocin baya Hoto: Bola Tinubu/Godswill Obot Akpabio
Asali: Facebook

Arise TV ta ruwaito cewa Akpabio ya ce jama’a su kwantar da hankulansu, domin gwamnati mai ci karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu na duk kokarinta wajen gyara tattalin arzikin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Gwamnatocin baya sun gaza:” Akpabio

Jaridar This day ta wallafa cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Apkabio ya ce gwamnatocin baya sun gaza daukar matakan da za su saita tattalin arziki.

Shugaban majalisar dattawan ya bayyana haka ne yayin kaddamar da littafi a kan aikata laifuka ta kafar intanet da binciken laifuffukan kudi a Abuja.

“Gwamnati za ta magance matsalar kasa:” Akpabio

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Apkabio ya ba yan kasar nan tabbacin cewa za a samu saukin matsalolin da jama’ar Najeriya ke fuskanta.

“Abubuwan da mu ke yi yanzu, mu na yi ne saboda kyautata gaba, ba saboda kawunanmu ba. Mu na ba ku tabbacin gwamnatin nan za ta bar ayyuka da za a mora a ga.”

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya bayyana babbar matsalar Najeriya da Tinubu ya fara magancewa

Yunwa: Akpabio ya ba yan kasa hakuri

A baya mun ruwaito cewa shugaban majalisar dattawan kasar nan, Godswill Akpabio ya roki yan Najeriya su kara hakuri da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu duk da yunwa da ake fama da ita.

Shugaban majalisar ya jaddada cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ya na kokarin gyara barnar tattalin arzikin kasa da barnar da tsohon gwamnan CBN ya yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.