Ana Raɗe Raɗin Wargajewa, Gwamna Abba Ya Tura Saƙo ga Kwankwaso

Ana Raɗe Raɗin Wargajewa, Gwamna Abba Ya Tura Saƙo ga Kwankwaso

  • A makon da ya wuce aka samu raɗe raɗin cewa za a samu baraka a tafiyar Kwankwasiyya saboda rikicin siyasa na cikin gida
  • Haka zalika an samu masu kiran Abba Kabir Yusuf ya tsaya da kafafunsa wanda hakan ke nufin cewa ya bijirewa madugunsu
  • Ana cikin haka, a safiyar Litinin, 21 ga Oktoba Abba Kabir Yusuf ya tura sakon taya murna ga Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tura sakon murnar ranar haihuwa ga Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.

Hakan na zuwa ne duk da yawaitar kiran cewa ya kamata Abba Kabir Yusuf ya bijirewa madugun Kwankwasiyya.

Kara karanta wannan

Gowon @90: Buhari ya yi yabo da tsohon shugaban kasa ya kara shekara a duniya

Kwankwaso
Abba ya taya Kwankwaso cika shekaru 68. Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya wallafa sakon da Abba Kabir Yusuf ya turawa Kwankwaso a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba ya taya Kwankwaso murna a ranar haihuwa

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya taya jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso murnar ranar haihuwa.

A ranar 21 ga watan Oktoban 2024 Sanata Rabi'u Kwankwaso ya cika shekaru 68 da haihuwa a duniya.

Gwamna Abba ya yi shekaru 38 tare da Kwankwaso

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa ya yi aiki tare da Rabi'u Kwankwaso a tsawon shekaru 38.

Haka zalika Abba Kabir Yusuf ya ce a tsawon shekaru, Kwankwaso ya nuna shi jarumi ne, mai gaskiya da taimakon al'umma. Ga abin da ya ce:

"Tsarin siyasarka ya kawo cigaba sosai ga al'umma, ya samar da shugabanni na gari ya kuma gina mutane a doron kasa.

Kara karanta wannan

"Kuna da damar taimakon ƴan Najeriya," Jigon APC ya dura kan Kwankwaso da Atiku

Lallai ka kasance madugu a siyasar Najeriya kuma kwararre a siyasar Arewa.
A madadin ni kaina, iyalaina, da al'ummar jihar Kano, muna maka fatan alheri. Allah ya kara maka shekaru masu albarka"

- Abba Kabir Yusuf, Gwamnan jihar Kano

Abba ya ba da N100m a Jigawa

A wani rahoton, mun ruwaito muku cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ba da tallafin N100m ga mutanen Jigawa.

Abba Kabir Yusuf ya yi kyautar ne bayan mutane sama da 150 sun rasu yayin mummunan hadarin tankar man fetur a Majia.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng