Ana Yada cewa Hafsan Sojoji na Fama da Matsanancin Jinya, An Fara Neman Kujerarsa

Ana Yada cewa Hafsan Sojoji na Fama da Matsanancin Jinya, An Fara Neman Kujerarsa

  • Rahotanni sun ba da labarin cewa hafsan sojojin Najeriya, Laftanar janar Taoreed Lagbaja yana fama da rashin lafiya
  • Hakan ya sanya wasu daga cikin manyan sojoji suka fara bin kafar yan siyasa da sarakuna domin maye gurbinsa
  • Sai dai rundunar sojojin ta ƙaryata labarin inda ta ce Lagbaja ya dauki hutu ne kuma babu wata matsala a shugabancinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Ana ta yada jita-jitar cewa hafsan sojojin Najeriya na fama da matsanancin rashin lafiya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Laftanar-janar Taoreed Abiodun Lagbaja na jinya a asibitin ketare.

Rundunar sojoji ta yi martani kan zargin rashin lafiyar hafsanta, Lagbaja
Ana yada cewa wasu sojoji sun fara bin kafa na muƙamin hafsansu saboda zargin rashin lafiya. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Twitter

Ana zargin hafsan sojoji ba shi da lafiya

Kara karanta wannan

DHQ: Dakarun sojoji sun cafke ƙasurgumin ɗan bindiga, sun hallaka wasu kusan 100

Vanguard ta ce wasu daga cikin manyan sojoji sun fara neman mukamin Lagbaja yayin da ya ke jinya a asibitin kasar waje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sahara Reporters ma ta tabbatar da cewa Lagbaja na cigaba da karbar kulawa kan wata cuta da ba a bayyana ba.

Majiyar ta ce akwai alamun cewa rashin lafiyar ta tsananta wanda ke saka fargaba a rundunar sojojin.

An samu bayanai daga wata majiya cewa an kwashe kimanin makwanni uku ba tare da ganin hafsan sojojin ba.

"Ina mai tabbatar muku da cewa Lagbaja yana fama da matsanancin rashin lafiya, iyalansa sun dauke shi zuwa asibitin ketare."
"A matsayinsa na shugaba, Manjo-janar da yawa suna yin abin da suka ga dama saboda babu wanda su ke kai rahoto gare shi."

- Cewar majiyar

Rundunar sojoji ta ƙaryata labarin

Sai dai mai magana da yawun rundunar, Manjo-janar, Onyema Nwachukwu ya ce Taoreed Lagbaja ya tafi hutu ne.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun bani: Sojoji za su samu jiragen yaki 50 domin zafafa luguden wuta

Nwachukwu ya ce babu wata matsala kan shugabancin Lagbaja a halin yanzu kamar yadda ake yadawa.

Lagbaja ya kore maganar juyin mulki

Kun ji cewa Hafsan sojojin kasa na Najeriya Laftanar Janar Taoreed ya ce sojoji ba za su yi sakaci a yi amfani da su wajen kifar da gwamnati ba.

Lagbaja ya ce duk da wasu manyan mutane sun nemi sojoji su kwace mulki amma ba za su yarda su kara zubarwa da kansu ƙima ba.

Shugaban sojojin ya ƙara nanata cewa babu wani dalili da zai sa su yi ƙoƙarin ruguza mutunci da ƙimar da suka gina tsawon shekaru 25 ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.