'Na Ware N1m', Mataimakin Gwamna Zai ba da Tukuici domin Kwamushe Mai Gidansa

'Na Ware N1m', Mataimakin Gwamna Zai ba da Tukuici domin Kwamushe Mai Gidansa

  • Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu ya sake taso mai gidansa a gaba kan zargin almundahana da kudin al'umma
  • Shaibu na zargin Gwamna Godwin Obaseki da karkatar da wasu kudi da kadarori yayin da yake shirin barin ofis nan ba jimawa ba
  • Mataimakin gwamnan daga bisani ya yi alkawarin ba da tukuicin kudi har N1m ga duk wanda ya kawo bayanai kan zargin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu ya zargi Gwamna Godwin Obaseki kan almundahana.

Shaibu ya zargi Obaseki da karkatar da kudaden al'umma yana daf da barin ofis cikin yan makwanni masu zuwa.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya bayyana babbar matsalar Najeriya da Tinubu ya fara magancewa

Mataimakin gwamna ya taso mai gidansa a gaba kan zargin almundahana
Mataimakin gwamnan Edo, Philip Shaibu ya ware N1m ga mai bayanai kan zargin badakalar Gwamna Godwin Obaseki. Hoto: Gov. Godwin Obaseki, Comrade Philip Shaibu.
Asali: Facebook

Shaibu ya bukaci EFCC ta binciki Obaseki

Punch ta ruwaito cewa Shaibu ya bukaci hukumar EFCC ta binciki gwamnan kan zargin sata da ya ke yi a yanzu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shaibu ya ba da tukuicin kudi har N1m kan duk wanda ya kawo bayanai kan almundahana da Obaseki yake yi.

Mataimakin gwamnam ya ce yana da hujjoji da zai kare kansa game da kwashe kudin al'umma da Obaseki ke yi yana da da barin ofis, cewar The Nation.

Philip na zargin bakuna da ba Obaseki basuka

"Ina samun wasu labarai marasa dadi kan zargin amincewa da basukan da wasu bankuna ke yi ga Gwamna Godwin Obaseki."
"Wannan abin takaici ne kuma ana yi ne ba da zuciya daya ba, ina gargadin duka bankuna da su yi hankali wurin ba Obaseki basukan ko wani jami'in gwamnati."

Kara karanta wannan

"A rage ciki:" Ministan Tinubu ya ce babu kudi a kasa, ya aikawa magidanta shawara

"Bayanai da nake samu sun tabbatar da cewa Obaseki zai kwashe kudin jihar ta hanyar amfani cibiyoyin da ba na gwamnati ba da niyyar taimakon al'umma."

- Philip Shaibu

Gwamna ya zargi Shaibu da mamaye gidan gwamnati

Kun ji cewa makwanni kadan bayan kammala zaben gwamnan Edo, gwamnatin jihar ta zargi mataimakin gwamna, Philip Shaibu da neman rigima.

Gwamnatin jihar ta zargi Shaibu ta shirya makarkashiya domin mamayar gidan gwamnati a ranar Litinin 30 ga watan Satumba.

Wannan na zuwa ne bayan kotu ta tabbatar da Shaibu a matsayin halastaccen mataimakin gwamnan jihar bayan tsige shi da aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.