'Yadda Mahaifinmu Ya Hana Mu Saka Rai a Gadonsa': Tsohon Gwamna Ya Magantu
- Tsohon gwamnan Osun ya bayyana yadda mahaifinsu ya gargade su kan arzikin da ya bari saboda ka da kowa ya saka rai
- Olagunsoye Oyinlola ya ce sun kasance su 64 a cikin iyalansu amma babu mai maganar rabon gadonsa har zuwa yanzu
- Oyinlola ya ce mahaifinsu wanda basarake ne kafin rasuwarsa ya ce babu wani gata da ya bar musu illa ilimi da suka samu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Osun - Tsohon gwamnan jihar Osun, Olagunsoye Oyinlola ya yi magana kan gadon gidansu.
Oyinlola ya ce mahaifinsu wanda basarake ne ya yi musu gargadi kan dogaro da arzikinsa ta hanyar gado.
Tsohon gwamna ya magantu kan wasiyyar mahaifinsu
Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne a taron wayar da kan dalibai a Kwalejin kiwon lafiya a Okuku da ke jihar, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Oyinlola ya ce mahaifinsu da ya rike sarautar Olokuku a garin Okuku ya shawarci 'ya'yansa 64 kan saka rai a arzikinsa.
Dan Sarkin ya ce marigayin ya fada musu cewa duk mai jiran ya ci gadonsa yana bata lokacinsa ne kawai.
Har ila yau, Oyinlola ya ce mahaifin nasu ya ce ya bar musu ilimi wanda shi ne gaban komai a rayuwa.
'Mahaifinmu ya gargade mu kan gadonsa ' - Oyinlola
"Lokacin da nake yaro kafin mahaifina wanda basarake ne ya rasu, ya ce duk mai jiran cin gadonsa yana bata lokacinsa ne."
"Ya ce babu abin da ya bar mana a matsayin yayansa 64 a rayuwa game da arziki ko gado da ya wuce ilimi."
"Har yanzu ilimi ne ke riƙe da gidanmu, yau shekaru 64 da mutuwarsa, babu wanda ya ke tunanin raba gado."
- Olagunsoye Oyinlola
Gwamna ya ce rawa na burge shi
Kun ji cewa Gwamna Ademola Adeleke na Osun ya ce yana ƙaunar rawa ne saboda tana faranta masa rai amma sauke nauyin talakawa ya fi masa daɗi.
Adeleke ya bayyana haka ne yayin da yake martani ga wani mutumi, wanda ya yaba da ƙoƙarin gwamnan duk da sukar da yake sha daga ƴan adawa.
Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa na ci gaba da gyaran asibitoci da gina hanyoyi a kowace ƙaramar hukuma a Osun.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng