Abinda yasa Obasanjo ya goyi bayan Buhari a 2015, Oyinlola

Abinda yasa Obasanjo ya goyi bayan Buhari a 2015, Oyinlola

- Tsohon gwamnan Oyo, Olagunsoye Oyinlola, ya bayyana dalilin da yasa Olusegun Obasanjo ya goyi bayan Shugaba Muhmmadu Buhari a 2015

- A cewar tsohon sakataren na PDP na kasa, Obasanjo ya goyi bayan Buhari ne saboda bai gamsu da abinda gwamnatin Jonathan ta ke yi ba

- Ya ce ko a lokacin Obasanjo ya san cewa Buhari ba zai tabuka wani abin azo a gani ba amma saboda yadda ta kasance da Jonathan sai ya goyi bayan Buhari

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya goyi bayan Muhammadu Buhari a shekarar 2015 duk da cewa ya san 'bai san komai ba' Olagunsoye Oyinlola, tsohon gwamnan jihar Osun ya ce.

Mista Oyinlola ya yi bayanin cewa Mista Obasanjo ya yanke shawarar goyon bayan Mista Buhari ne saboda takaicin gwamnatin Goodluck Jonathan.

DUBA WANNAN: Dan majalisar APC ya bindige ɗan fashi da makami har lahira a Sokoto

Abinda yasa Obasanjo ya goyi bayan Buhari a 2015, Oyinlola
Abinda yasa Obasanjo ya goyi bayan Buhari a 2015, Oyinlola. Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

Duk da cewa (shi) Obasanjo ya san cewa dan takarar na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ba zai iya tabuka wani abin azo-a-gani ba, amma duk da haka ya goyi bayansa bayan wasu jiga-jigan yan Najeriya sun matsa masa lamba.

Mista Oyinlola, wanda ya taba rike mukamin sakataren jam'iyyar PDP na kasa, ya yi wannan jawabin ne a wata hira da ya yi da The Punch.

KU KARANTA: Sule Lamido: Saboda Buhari ake tsangwamar Fulani a Nigeria

"Mutum na karshe da ya amince da Buhari shine Obasanjo kuma ina da tabbacin haka saboda ina cikin tawagar. Eh, Baba (Obasanjo) ya samu matsala da Jonathan. A lokacin zai amince da kowanne zabi amma banda Jonathan," in ji wannan shine matsayansa.

"Idan aka yi la'akari da yan takarar da sauran jam'iyyun suka tsayar, babu wanda zai iya mulkar Najeriya fiye da yadda Buhari zai yi a lokacin. Shi yasa aka goyi bayan Buhari.

"Bayan haka, duba da cewa ya taba rike shugabancin kasar a karkashin mulkin soja, don haka ya fi sauran ta wannan bangaren. Amma Baba Obasanjo shine na karshen amincewa ya marawa Buhari baya."

Oyinlola ya ce shi da su Saraki, Amosun, Bola Tinubu, Kashm, Imam suka tafi wurin Baba (Obasanjo) a gonar Ota da karfe bakwai na safe kafin ya amince.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NANbhoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel