Sojojin Najeriya Sun Kashe Shugabannin Yan Ta’adda bayan Fafatawa

Sojojin Najeriya Sun Kashe Shugabannin Yan Ta’adda bayan Fafatawa

  • Rundunar tsaron Najeriya ta sanar da gagarumar nasarar da ta samu kan yan ta'adda a Arewaci da Kudancin kasar nan
  • A yankin Arewa maso Yamma, dakarun sojin Najeriya sun kama wasu yan bindiga da dama kuma sun kubutar da mutane
  • Haka zalika a Kudu maso Gabas, sojojin sun hallaka shugabannin yan ta'addar IPOB da kungiyar ESN da ke matsawa jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rundunar tsaron Najeriya ta fitar da sanarwa kan wasu miyagu yan bindiga da ta hallaka a kasar nan.

Cikin yan ta'addar da sojojin Najeriya suka samu nasarar kashewa akwai wasu daga cikin shugabannin kungiyar IPOB da ESAN.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gano gidan da yan bindiga ke boye makamai, an kama mata da miji

Sojoji
Sojoji sun kashe shugabannin yan ta'adda. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Twitter

Jaridar The Nation ta wallafa cewa sojojin sun kama wasu tarin yan ta'adda a sassa daban daban na kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dakarun Sojoji sun ceto mutanen da aka sace

Daraktan yada labaran rundunar tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba ya sanar da cewa sun ceto mutane 157.

Mutane 157 da rundunar da ceto galibi an kwato su ne a hannun masu garkuwa da mutane bayan an fafata da yan bindiga.

"Sojoji sun kashe yan ta'addan IPOB" - DHQ

A Kudancin Najeriya, rundunar tsaro ta sanar da samun nasara kan wasu daga cikin shugabannin yan ta'addar IPOB da ESN.

Manjo Janar Edward Buba ya bayyana cewa sun hallaka hudu daga cikin shugabannin yan ta'addar da suka fitini yankin.

Sojoji za su cigaba da sakin wuta

Jaridar Punch ta wallafa cewa Manjo Janar Edward Buba ya tabbatar da cewa za su cigaba da sakin wuta kan yan bindiga a Najeriya.

Kara karanta wannan

An canza salo: Gwamnatin Najeriya ta fitar da bayanai kan yi wa yan bindiga tarko

Ya ce za su cigaba da kai farmaki kan yan bindiga da lalata maboyarsu a dukkan sassan Najeriya har sai sun gama da su.

An kama wanda ya kashe yan mata

A wani labarin, mun ruwaito muku cewa yan Amotekun a jihar Ogun sun cafke wani matashin mai suna Ogunnaike Philip bisa zargin kisan kai.

Yan Amotekun suna zargin Ogunnaike Philip ne da kashe wasu yan mata uku da kuma wulaƙanta gawarsu a wani kango.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng