An Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Ya Kashe Mata, Ya Wulaƙanta Gawarsu
- An kama wani ƙasurgumin ɗan bindiga mai suna Ogunnaike Philip a jihar Ogun da zargin ya hallaka wasu yan mata guda uku
- Ana zargin cewa Ogunnaike Philip ya kashe yan matan, ya wulaƙanta gawarsu har sai da suka fara ruɓewa bayan wurgar da su
- Rahotanni sun ce ana zargin wannan mutum ya shahara da kashe rayukan da ba su ji ba, ba su gani ba a yankuna da dama a Ogun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Ogun - Yan Amotekun a Kudu maso Yamma sun kama wani dan bindiga da ake zargi da kisan wasu mata.
Ana zargin cewa Ogunnaike Philip ya yi wa wasu yan mata ne kisan gilla kuma ya wulakanta gawarsu.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa jami'in yada labaran Amotekun, Adeleye Abiodun Adewale ne ya fitar da sanarwar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dan bindiga ya kashe yan mata
Dakarun Amotekun a jihar Ogun sun kama wani matashi mai shekaru 29 bisa zargin kisan gilla wa wasu yan mata uku.
Ana zargi Ogunnaike Philip ya kashe yan matan ne a jihar Ogun a lokuta mabanbanta ciki har da wata budurwa mai shekaru 18.
Yadda aka gano matan da aka kashe
Yan Amotekun sun bayyana cewa an samo gawar wata budurwa mai suna Taiwo ne a wani jeji a kusa da unguwar Egbewa a cikin wani kango.
Haka zalika an samo gawar daya budurwar mai suna Fatoki Seun a wani jeji kusa da unguwar Oki-Oja a jihar.
Rahotanni sun nuna cewa yan Amotekun sun samo gawar yan matan ne bayan sun fara ruɓewa a wajen da ake tunani an wurgar da su.
An mika gawar yan mata a asibiti
Daily Post ta wallafa cewa yan Amotekun sun ce a yanzu haka an mika gawar yan matan a babban asibitin yankin.
Kakakin Amotekun, Adeleye Abiodun Adewale ya bayyana cewa dan bindigar ya shafe wata daya a yankin kafin a gano barnar da ya yi.
Za a fadada yaki da yan bindiga
A wani rahoton, kun ji cewa ministan tsaron Najeriya, Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana shirin yakar yan bindiga da suka yi.
Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana shirin ne yayin ganawa da gwamnan jihar Kaduna domin neman hadin kan shugabannin Arewa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng