Sojoji Sun Gano Gidan da Yan Bindiga ke Boye Makamai, an Kama Mata da Miji

Sojoji Sun Gano Gidan da Yan Bindiga ke Boye Makamai, an Kama Mata da Miji

  • Rundunar sojin Najeriya ta cafke wasu mutane a jihar Taraba da ake zargin suna hada kai da yan bindiga masu garkuwa da mutane
  • Kakakin rundunar soji a jihar Taraba, Kyaftin Oni Olubo ya tabbatar da cafke mutanen da ake zargin a ƙaramar hukumar Lau
  • Kyaftin Oni Olubo ya bayyana rawar da yan Najeriya za su iya takawa wajen taimakawa jami'an tsaron kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Taraba - Rundunar sojin Najeriya ta cafke wasu mutane uku da ake zargi da taimakawa yan bindiga masu garkuwa da mutane.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an kama mutanen ne a karamar hukumar Lau ta jihar Taraba a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

An canza salo: Gwamnatin Najeriya ta fitar da bayanai kan yi wa yan bindiga tarko

Sojoji
Sojoji sun kama masu boyewa yan bindiga makamai. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa kakakin rundunar soji ta shida, Kyaftin Oni Olubo ne ya fitar da sanarwar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan bindiga: Sojoji sun kama mata da miji

Rundunar sojin Najeriya ta kama wasu mutane uku da ake zargi da taimakon yan bindiga a jihar Taraba.

Cikin mutanen akwai mata da miji da wani mutum da suke aiki tare wajen boyewa yan bindiga makamai.

Rahoton Radio Nigeria ya nuna cewa an kama mutanen ne a kauyen Lande Jessy a ƙaramar hukumar Lau ta jihar Taraba.

Yadda aka kama mata da miji a Taraba

Kakakin rundunar sojin Najeriya a Taraba, Kyaftin Oni Olubo ya ce bayan samun bayanan sirri a kan mutanen ne suka bi diddiginsu.

Biyo bayan haka aka kama mutanen, kuma sun tabbatar da cewa idan yan bindiga suka fita ta'addanci suka dawo sai su ajiye musu makamai.

Kara karanta wannan

An cafke barayin babur da suka sassara dattijo ɗan shekaru 60 da adda

Sojoji sun yi kira ga al'ummar Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta yi kira kan cigaba da samar mata da bayanan sirri kan yan bindiga domin kawo karshensu a kasar nan.

Kyaftin Oni Olubo ya ce rundunar sojin Najeriya za ta cigaba da ƙoƙarin tabbatar da tsaron al'ummar kasar nan.

Najeriya za ta yi haɗaka da Nijar

A wani rahoton, mun ruwaito muku cewa gwamnatin Najeriya za ta yi haɗaka da kasar Nijar domin cigaba da farautar yan bindiga.

Ministan tsaron Najeriya, Muhammad Badaru Abubakar ne ya bayyana haka bayan ganawa da gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng