Satar Wayoyi 100 Ta Jefa Wasu Dalibai a cikin Matsala, 'Yan Sanda Sun Yi Bayani
- Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta cafke wasu dalibai biyu ‘yan shekara 15 Hamza Sadiq da Adamu Ahmadu bisa zargin satar wayoyi
- Wadanda ake zargin sun amsa laifinsu, inda suka bayyana yadda suka shiga shagon da suka yi satar a lokacin da mai shagon ya fita
- Rundunar ‘yan sandan ta kwato wayoyin hannu 21 da wasu kayayyakin da aka sace, inda ta bayyana cewa za a tura yaran gidan kurkuku
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Bauchi - A wani lamari mai matukar tayar da hankali, rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wasu daliban makarantar sakandare biyu, 'yan shekaru 15.
An ce 'yan sanda sun cafke yaran ne bisa zargin satar wayoyin hannu 100 da wasu na’urorin lantarki a wani shagon sayar da wayar hannu da ke Bauchi.
An bayyana sunayen wadanda ake zargin da Hamza Sadiq da Adamu Ahmadu, daliban makarantar sakandare ta Bakari Dukku, inji rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kama daliban sakandare 2
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, SP Ahmed Wakil, ya bayyana cewa an kama su ne biyo bayan rahoton wani mai shago da ya ce an tafka masa sata.
Wakili ya ce:
"A ranar 1 ga Oktoba, 2024, wani mai shagon sayar da wayar hannu ya ba da rahoton satar wayoyin hannu 100, na'urar MP4 75, batirin waya 30, na'urar ajiyar bayanai (M-Cards) 50, da na'urar Bluetooth ta kunne."
Nan take kwamishinan ‘yan sanda, Auwal Musa, ya umarci rundunar ‘Operation Restore Peace (ORP)’ karkashin jagorancin CSP Kim Albert, da su binciki zargin.
Sanarwar ta ce kokarin da suka yi ya sa aka kama daliban biyu cikin karamin lokaci.
Daliban sun amsa laifin sata
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa a yayin da ake yi musu tambayoyi, wadanda ake zargin sun amsa aikata laifin satar wayoyin.
Sun yi bayanin kan yadda suka samu makullin shagon da karantar lokacin da mai shagon ba ya zama, sannan da yadda suka rika shiga shagon suna sace kayayyakin.
“Wadanda ake zargin sun amsa laifin sayar da wayoyin da suka sace a kan farashin N5,000 zuwa N8,000.
“Sun ce sun yi amfani da kudin ne wajen sayan tufafi, abinci, har ma da wayar salula, wadda daga baya aka sace ta daga hannun daya daga cikinsu."
- Inji Ahmed Wakili.
'Yan sanda sun cafke dalibin ATBU
A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar 'yan sandan Bauchi ta cafke wani dalibin jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke jihar kan zargin mallakar bindiga.
SP Ahmed Wakil, mai magana da yawun rundunar yan sandan Bauchi ya ce an kama Mike James Habila da bindiga biyu kirar gida Najeriya da kuma harsashi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng