Abun kunya: Saurayi ya yi satar wayoyi da jaka a gidan sirikai

Abun kunya: Saurayi ya yi satar wayoyi da jaka a gidan sirikai

- 'Yan sandan jihar Legas na jiran wani saurayi mai shekaru 29 a duniya ya samu lafiya a hukuntashi

- Ana tuhumarsa ne da laifin sata da kuma yunkurin kashe kansa

- Saurayin ya sha omo ne bayan da sojoji sirikansa suka biyosa har gida don karbar wayoyin da ya sace a ziyarar da ya kai musu

'Yan sanda zasu gurfanar da Olusegun Ogunleye mai shekaru 29, na lamba 16 titin Idahosa, Ajao Estate da ke Legas da laifin sata da yunkurin kisan kai, a lokacin da lafiyarsa ta samu.

Olusegun ya shanye omo kwano daya ne bayan da sojoji suka rako budurwarsa, Blessing Gotam da dan uwanta Peter Gokat gidansa don karbar wayoyi biyu da jakunkunan da ake zargin ya sata a ziyarar da ya kaiwa budurwar a Epe.

Majiyar ta ce, bayan Olusegun ya sha omon sai ya suma, a take kuwa aka kwashesa sai asibiti don ceto rayuwarsa.

KU KARANTA: Bakin-talauci-ya-sanya-ikechukwu-azumin-kwanaki-41-ji-mahaifiyarsa

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Olusegun na da ciwon koda kuma wannan dalilin ne yasa mahaifiyarsa, Victoria Ogunleye komowa Ajao Estate don kula da shi.

Majiyar ta ce, "Olusegun ya kai ziyara Epe inda ya yi kwanaki 3 tare da Gotam da dan uwanta. A ranar Litinin, Gotam, dan uwanta da matarsa sun tafi wajen aiki suka bar Olusegun a gida. Ya kira Gotam cewa zai tafi da wayoyi biyu, daya kirar infinix da zata iya kaiwa N46,000 sai Tecno da zata kai N23,000,"

Majiyar ta kara da cewa, "Ya sanar da budurwar ta sa cewa zai tafi da jakarta wacce ta kunsa kayan sawa, turaruka, mai da sauran kayan kwalliya. Amma sai ta rokesa da kada ya dau wayoyin don daya daga ciki ta wajen aikin matar Gokat ne,"

"Bayan makonni biyu, dan uwan Gokat wanda soja ne, ya rakasa don karbo wayoyin inda suka hadu da Olusegun a hanya. Sun rankaya gida don dauko wayoyin inda suka tarar da mahaifiyarsa. A take ta sanar dasu cewa ta umarcesa da ya maida wayoyin amma yaki," in ji majiyar.

Kamar yadda majiyar ta sanar "Haushin hakan yasa ya shiga daki tare da rufe kansa inda ya shanye kwanon omo."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng