'Yana Yawo cikin Dare,' Sanata Ya Tona Yadda Tinubu Yake Zagaya Gari a Boye

'Yana Yawo cikin Dare,' Sanata Ya Tona Yadda Tinubu Yake Zagaya Gari a Boye

  • Orji Uzor Kalu ya yi albishir ga yan kasar nan kan samun saukin matsin rayuwa da tsadar kayan amfanin yau da gobe
  • Sanatan mai wakiltar Abia ya ce shugaban kasa kan yi rangadi lokaci zuwa lokaci domin ganewa idanunsa halin da ake ciki
  • Ya kara da cewa ba kasar nan kawai ke fama da talauci da kuncin rayuwa ba, sauran kasashe na fama da irin matsalolin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar Abia ta Arewa, Orji Kalu ya ce shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya na sane da halin da Najeriya ke ciki.

Kara karanta wannan

'Alamar matsala tsakanin Tinubu da Shettima,' Hadimin Osinbajo ya fito da bayanai

Sanata Orji Kalu ya bayyana cewa shugaban kasa na bibiya, kuma ya kan fito da tsakar dare ya yi rangadi a babban birnin tarayya.

Bola Ahmed
An fadi yadda Tinubu ke yawon dare don ganin yadda jama'a ke rayuwa Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar The Cable ta tattaro cewa Bola Ahmed Tinubu ya damu matuka da wahalar da ake sha a Najeriya, kuma ya na bakin kokarinsa wajen magance ta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Duk duniya ana shan wuya:" Sanata Kalu

Tashar Channels Television ta wallafa cewa Sanata mai wakiltar Abia ta Arewan ya ce ba a kasar nan ne kawai ake fama da matsin rayuwa ba.

Sanata Orji Kalu ya dora alhakin wahalar da ake gani a duniya kan annobar COVID-19 da ta durkusar da tattalina arzikin kasashe masu tasowa.

Sanata ya ce ana kokarin yaye talauci

Orji Kalu na ganin matakan da gwamnatin tarayya ta bijiro da su a kasar nan za su warware matsalolin tattalin arziki..

Kara karanta wannan

"A rage ciki:" Ministan Tinubu ya ce babu kudi a kasa, ya aikawa magidanta shawara

Ya ce Bola Tinubu ba kifin rijiya ba ne, ya na fita domin ganin halin da jama'a su ke ciki, kuma zai yi abin da ya dace wajen warware matsalolin.

"Manufofin Tinubu ba su da amfani" - Sanata Sani

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani na ganin manufofin farfado da tattalin arziki da gwamnatin Bola Tinubu ke amfani da su na da matsala.

Ya bayyana cewa manufofin na kara jefa jama'ar Najeriya a cikin kan talauci, saboda haka ya ga laifin Bankin Duniya da ya bayar da shawarar a cigaba da amfani da tsarin na wasu shekaru 15.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.