FCTA: Wike Ya Kaddamar da Rusa Gidajen Mutane a Abuja, Bayanan Rusau Sun Fito
- Hukumar gudanarwar birnin tarayya Abuja, karkashin jagorancin Nyesom Wike ta fara rusa gidajen da aka gina ba bisa ka'ida ba
- Mukhtar Galadima, wani jami'i a hukumar FCTA, ya sha alwashin cewa hukumar za ta ci gaba da kakkabe haramtattun gine-gine
- A zantawarmu da wani mai zane da gina gidaje a Abuja, Abdullahi Rabiu Sani, ya ce rusa gidajen da FCTA ke yi maslaha ce ga al'umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar FCTA karkashin jagorancin Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya (FCT) ta kaddamar da rusau a wasu sassan Abuja.
Bisa umarnin Nyesom Wike, an ce hukumar FCTA ta kaddamar da rusau a Sabon Lugbe, inda za a rusa wasu gidaje 50 da aka gina ba bisa ka'ida ba.
Mukhtar Galadima, daraktan sashen kula da ci gaban birnin ne ya jagoranci aikin a ranar Alhamis, 17 ga watan Oktoba, inji rahoton Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
FCTA ta magantu kan 'Abuja Phase 5'
Jami'in hukumar ya jaddada cewa masu kwacen filaye sun gina wadannan gine-gine ba tare da amincewar hukumomin da suka dace ba.
Galadima ya fayyace cewa yankin Kudu maso Yamma na Sabon Lugbe ya fada cikin gundumar Phase 5 na babban birnin tarayya (FCC).
Ya yi gargadin cewa hukumar za ta dakile masu satar fili sannan ya shawarci masu son saye da su tabbatar da sahihancin kadarori kafin biyan kudi.
Hukumar FCTA za ta rusa gidaje 50 a Abuja
A cewar jaridar Tribune, an fara rusau din ne da gine-gine 10, inda Galadima ya sha alwashin ci gaba da aiwatar da aikin.
"Gobe za mu dawo da karfinmu. Za mu tabbatar da cewa an rushe duk wasu gine-ginen da aka yi ba bisa ka'ida ba, kusan gidaje 50 za mu rusa."
- A cewar Galadima.
Galadima ya lura cewa masu satar filaye suna yaudarar mazauna wurin cewa za a shigar da wadannan yankuna cikin Phase 5 na FCC.
'Rusa gidajen ya fi fa'ida ga al'umma' - Abdullahi
A zantawarmu da masani kan harkar gine-gine, Arch. Abdullahi Rabiu a Abuja, ya ce rusa gidajen a wannan lokaci ya fi fa'ida ga al'umma musamman wadanda ke ciki.
Wanda ke cikin harkar zane da gina gidajen ya ce duk wani gida da za a rusa ya sabawa ka'idar gini ko kuma ya yi lalacewar da zai iya rushewa a kowane lokaci.
Arch. Abdullahi Rabiu a Abuja, ya ce ana samun yawaitar rushewar gine-gine wanda ke jawo asarar rayuka saboda wasu dalilai da dama.
Ya ce ana iya samun kuskuren farko daga wanda ya zana gidan, yana mai cewa kura-kurai a wajen kayyade adadin nauyin da gini zai iya dauka na jawo ruftawarsa.
Mai zanegidan ya ce idan ba a samu matsala daga zane ba, to ana iya samun matsala daga wadanda za su yi ginin, walau kin bin tsarin zanen, ko amfani da kayan aiki marasa kyau.
Abuja: Wike zai rusa gidaje 6,000?
A wani labarin, mun ruwaito cewa ministan birnin tarayya, Nyesom Wike, ya yi watsi da rahotannin da ke cewa zai fara aikin rusa gidaje 6000 a fadin unguwanni 30 a Abuja.
A yayin da ya nuna bukatar rusa gidajen da aka gina su ba bisa ka'ida ba, Wike ya kuma nanata cewa ba zai iya gyara Abuja a cikin kwanaki shida ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng