Ana Fafutukar Kara Jihohi a Arewa, 'Yan Majalisa Na Son Kirkiro Sabuwar Jiha a Kudu

Ana Fafutukar Kara Jihohi a Arewa, 'Yan Majalisa Na Son Kirkiro Sabuwar Jiha a Kudu

  • Majalisar wakilan kasar nan ta sake waiwayar kudurin da Hon. Godwin Offiono ya gabatar gabanta kan kirkiro jiha
  • Hon. Godwin Offiono ya nemi majalisa ta amince da kirkiro jihar Ogoja daga jikin Cross Rivers da ke Kudu maso Kudu
  • A zaman majalisar wakilai na ranar Alhamis, kudurin ya tsallake karatu na biyu, Offiono ya fadi amfanin samar da jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa

Jihar ross Rivers - Dan majalisa mai wakiltar mazabar Ogoja/Yala, Godwin Offiono ya kusa cimma muradinsa da samun amincewar majalisar wakilai domin kirkiro sabuwar jiha.

Hon. Godwin Offiono na neman majalisa ta amince a yi wa sashe na takwas na kundin tsarin mulkin kasa kwaskwarima.

Kara karanta wannan

"Za a samu matsala:" Majalisa ta hango barazanar tashin hankali kan tsadar fetur

Majalisa
Kudirin kirkiro jihar Ogoja ya tsallake karatu na 2 Hoto: House of Representatives
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa dan majalisar na fatan a samar da sabuwar jiha da za a sa wa suna Ogoja a yankin Kudu maso Kudu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne a lokacin da ake fafutukar a kirkiro jihohi biyu - Ghari da Tiga daga jihar Kano da ke Arewacin kasar nan.

Ana neman samar da jihar Ogoja a Majalisa

Jaridar The Cable ta wallafa cewa kudurin kirkiro sabuwar jihar Ogoja ya tsallake karatu na biyu a majalisar wakilai.

Dan majalisar da ya gabatar da kudirin a gaban majalisa tun da fari, ya ce akwai dalilai da dama da ke nuna bukatar a samar da jihar.

Dalilin fafutukar samar da jihar Ogoja

Hon. Offiono ya bayyanawa majalisar wakilai dimbin alfanun da ke tattare da tabbatar da kafa sabuwar jihar Ogoja a yankin.

Kara karanta wannan

Bayan rasa rayuka a Jigawa, barci ya dauke direba, wata tankar fetur ta kama da wuta

Kadan daga cikin amfanin da ya lissafo akwai cin moriyar manyan kayan noma kamar su Cocoa, gyada da bishiyar roba da sauran albarkatun karkashin kasa.

Majalisa ta dubi kudirin kirkiro sabuwar jiha

A wani labarin, mun ruwaito cewa kudirin samar da sabuwar jiha a shiyyar Kudu maso Gabas ya tsallake karatu na farko a majalisar wakilai.

'Yan majalisar wakilai biyar daga jihohin yankin Abia, Imo, Enugu, Anambra da Ebonyi ne suka gabatar da kudirin kafa jiha mai suna Etiti.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.