Ta Faru Ta Kare, Gwamnatin Tinubu Ta Kawo karshen Tallafin Canjin Kudi da Na Fetur

Ta Faru Ta Kare, Gwamnatin Tinubu Ta Kawo karshen Tallafin Canjin Kudi da Na Fetur

  • A ranar Alhamis ne gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta sanar da kawo karshen tallafin fetur da na canjin kudi
  • Ministan kudi da tattalin arziki, Wale Edun ya bayyana cewa wadannan tallafin sun lakume sama da Naira Tiriliyan 10 na kasar
  • Hakazalika, Wale Edun ya ce gwamnatin Tinubu ta dauki matakai da su kawo karshen radadin rashin ayyukan yi a kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A hukumance, gwamnatin tarayya ta sanar da kawo karshen tallafin man fetur da na musayar kudaden waje.

Ayyana dakatar da tallafin ya kawo karshen ce-ce-ku-cen da ake yi kan tsare-tsaren gwamnatin Bola Tinubu na tallafin.

Kara karanta wannan

Bankin duniya ya ba gwamnatin Tinubu shawara kan maido tallafin man fetur

Gwamnatin tarayya ta yi magana kan kawo karshen tallafin fetur da na canjin kudi
Gwamnatin Bola Tinubu ta kawo karshen tallafin fetur da na canjin kudi a hukumance. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Ministan kudi da tattalin arziki, Wale Edun ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis 17 ga watan Oktoba kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"An kawo karshen tallafi" - Minista

Wale Edun, ya yi maganar ne a lokacin da ya ke gabatar da makala a taron da Bankin Duniya ya gabatar kan shirin bunkasa Najeriya a Abuja.

Ministan ya bayyana cewa wadannan tallafin sun durkusar da tattalin arzikin kasar.

Edun ya ce tallafin da gwamnati ta kawo sun lakume sama da Naira Tiriliyan 10, wanda ya kai 5% na jimillar karfin tattalin arzikin Najeriya.

"An kawo karshen tallafin man fetur da canjin kudaden waje,"

Edun ya shaidawa duniya wannan yayin da ya jaddada matsalar kudi da wadannan manufofin suka sanya wa al'umma.

Tinubu zai rage radadin rashin ayyukan yi

Ministan ya kuma bayyana wani sabon shiri na gwamnatin Bola Tinubu da ke da nufin magance radadin rashin ayyukan yi, wanda zai mayar da hankali kan gidaje.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya bayyana babbar matsalar Najeriya da Tinubu ya fara magancewa

Kamar yadda ya yi bayani, wannan yunkurin zai kunshi tsarin ba da jinginar gida wanda kuma zai zo a riba kankanuwa ga masu sha'awar shiga tsarin.

Gwamnatin Shugaba Tinubu na sa ran wannan tsarin zai bunkasa ayyukan gine-gine da samar da gagarumin aikin yi a fannin.

Shirye shiryen tallafi 11 da shafukansu

A wani labarin, mun ruwaito cewa Bola Ahmed Tinubu ya fitar da wasu shirye shirye na tallafawa ‘yan Najeriya a bangarori daban-daban.

Daga cikin shirye shiryen akwai shirin ba da lamunin mallakar gida, shirin ba da tallafi ga matasa masu fikira (NATEP) da dai sauransu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.