CNG: Gwamnati Ta Bayyana Abin da Ya Jawo wata Mota Mai Amfani da Gas Ta Fashe

CNG: Gwamnati Ta Bayyana Abin da Ya Jawo wata Mota Mai Amfani da Gas Ta Fashe

  • Gwamnati ta yi martani yayin da wani bidiyo da ya bazu a intanet ya nuna lokacin da wata mota mai amfani da CNG ta fashe a Edo
  • A cikin wata sanarwa, hukumar kula da shirin shugaban kasa na PCNGI ta bayyana fashewar motar a matsayin "abin takaici"
  • PCNGI ta kuma yi cikakken bayani game da dalilin fashewar motar inda kuma ta aika da sakon jaje ga wadanda suka jikkata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Edo – Hukumar kula da shirin shugaban kasa na PCNGI ta yi martani kan wani iftila'i da ya faru da wata mota mai amfani da gas a jihar Edo.

Hukumar PCNGI ta bayyana fashewar da motar ta yi a wani gidan man CNG da ke garin Benin a matsayin "abin takaici".

Kara karanta wannan

CNG: Ana jimamin hatsarin Jigawa, mota mai amfani da gas ta fashe a gidan mai

Gwamnatin Najeriya ta yi magana kan motar CNG da ta fashe a jihar Edo
Gwamnatin Najeriya ta ce an yi amfani da bututu marar kyau a motar CNG da ta fashe a Edo. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Gwamnati ta yi martani kan fashewar mota

Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da shirin shugaban kasar na samar da gas din CNG ya fitar a shafinsa na X a ranar Alhamis, 17 ga watan Oktoba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mahukuntan shirin PCNGI sun bayyana cewa lamarin ya shafi wata mota da aka rikidar da ita daga fetur zuwa CNG ba bisa ka'ida ba, kuma abin ya faru ne a gidan man NIPCO.

Mahukuntan shirin sun kuma ce babu asarar rayuka a fashewar motar yayin da ta mika sakon jaje ga wadanda suka jikkata.

'Yan sanda na binciken fashewar' - PCNGI

PCNGI ta kuma lura cewa akwai bukatar ayi taka-tsan-tsan da dukkanin wasu kayayyaki da ake sarrafa su da sinadarin hydrocarbons domin kare rayuka.

Sanarwar ta ce:

"Binciken da aka yi ya nuna cewa bututun gas din da ke cikin motar da ta fashe a Benin City anyi masa walda ne kuma an hada shi ne ba bisa ka'ida ta amfani da gas din CNG ba.

Kara karanta wannan

"Allah ji ƙansu," Gwamnan Abba ya yi maganar mutuwar sama da mutum 100 a Jigawa

"Yan sanda da hukumomin gwamnati da kuma hukumar NIPCO suna gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin kuma akwai hadin kai a tsakanin hukumomin”.

Bugu da kari kuma, PCNGI ta ce lamarin ya sake nanata kwarin guiwar fasahar sa ido kan ababen hawa masu amfani da gas na Najeriya da za a kaddamar nan ba da dadewa ba.

Motar CNG ta fashe a gidan mai

Tun da fari, mun ruwaito cewa wata mota da ke amfani da iskar gas na CNG ta fashe a gidan man NIPCO da ke Aduwawa kan babbar hanyar Benin zuwa Auchi a ranar Alhamis.

Wani faifan bidiyo da aka yi ta yaɗawa a shafukan sada zumunta, an nuna yadda motar ta yi raga-raga bayan aukuwar fashewar lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.