Tsadar Fetur: Yadda Gwamnatin Tinubu Ta yi wa Yan Kwadago Sababbin Alkawura

Tsadar Fetur: Yadda Gwamnatin Tinubu Ta yi wa Yan Kwadago Sababbin Alkawura

  • Gwamnatin tarayya ta yi zama da kungiyoyin kwadago domin tattaunawa kan karin kudin man fetur da albashin ma'aikata
  • Tun bayan karin kudin fetur yan kwadago suka rika cewa karin albashi da aka yi zuwa N70,000 ba zai yi wani amfani ba
  • Legit ta zanta da wani ma'aikaci, Muhammad Babayo Aliyu domin jin yadda ya dauki alkawarin samun sauki da aka musu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi wa yan kwadago alkawura biyo bayan karin kudin man fetur da aka yi.

Gwamnatin tarayya ta ce za ta gyara matatun man Najeriya domin kawo saukin rayuwa a kasar nan.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya bayyana babbar matsalar Najeriya da Tinubu ya fara magancewa

Tinubu
Tinubu ya yi wa yan kwadago alkawura. Hoto: Nigeria Labour Congress HQ|Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Vanguard ta wallafa cewa gwamnatin tarayya za ta tabbatar dukkan jihohin Najeriya sun yi karin albashi zuwa N70,000.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati za ta samar da motocin CNG a jihohi

Gwamnatin tarayya ta ce cikin matakan da za ta dauka a akwai samar da motocin CNG a jihohi domin saukaka zirga zirga.

A cewar gwamnatin, za ta tattauna da gwamnoni domin tabbatar da hakan kuma za a samu saukin dauko kaya daga waje zuwa waje.

Maganar biyan albashin N70,000

A wani ɓangaren, gwamnatin tarayya ta ce za ta tabbatar da cewa gwamnonin jihohi sun yi karin albashi a karshen watan Oktoba.

A karkashin haka, gwamnatin tarayya za ta gayyaci gwamnonin jihohi wata tattaunawa domin tabbatar da karin albashi a kan lokaci.

NLC za ta shiga kwamitin tattali

Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin cewa za a saka yan kwadago cikin kwamitin tattalin arzikin kasa.

Kara karanta wannan

Gwamnati za ta dauki mataki bayan gano masu ɗaukar makamai, su aikawa miyagu

Hakan zai taimaka wajen ba yan kwadago damar shiga tattauanawa kan tsare tsaren tattalin arzikin Najeriya.

Sauran alkawuran sun hada da gyaran matatun man Najeriya cikin gaggawa da biyan hakkokin ma'aikata da aka rike.

Legit ta tattauna da ma'aikaci

Wani ma'aikacin gwamnati ya bayyanawa Legit cewa ba lallai alkawuran da aka yi wa yan kwadago su cika ba.

Muhammada Babayo Aliyu ya ce babu wani tsammani da za su yi sai dai kawai idan suka ga abin kirki ya faru su yi farin ciki.

Za a rabawa yan Najeriya kudi ta banki

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta yi alkawarin fara turawa yan Najeriya kudi ta asusun bankuna domin rage radadi.

Ministan kudi, Wale Edun ya bayyana cewa kimanin talakawan Najeriya miliyan 20 ne ake saka ran za su ci moriyar shirin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng