Gwamnan APC Ya Gwangwaje Hazikan Ma'aikata 82 da Kyautar Naira Miliyan 42
- Gwamnan Ekiti, Biodun Oyebanji ya mikawa ma’aikata 82 kyautar tsabar kudi Naira miliyan 42 saboda kwazon da suka nuna a aiki
- A yayin wani taron kungiyar ma’aikatan gwamnati, Oyebanji ya yi wa ma’aikata alkawari kan biyan sabon mafi karancin albashi
- Gwamnan ya kuma yaba wa ma’aikatan bisa hakurin da suka nuna, ya yi alkawarin cewa nan ba da dadewa za su ci gajiyar hakan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ekiti - Gwamna Biodun Oyebanji na Ekiti ya jaddada kudirin gwamnatinsa na bayar da lada mai tsoka ga hazikan ma’aikatan jihar.
Mai girma gwamnan ya kuma kara jaddada kudurinsa na ganin ma'aikatan jihar sun samu sabon mafi karancin albashi.
Gwamna Oyebanji ya ba ma'aikatar kyautar kudi
Biodun ya bayar da wannan tabbacin ne a yayin taron kungiyar ma'aikatan gwamnati da bayar da lambar yabo ta 2024 da aka gudanar a Ado Ekiti, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taron da aka gudanar a ranar Talata, 15 ga Oktoba wani bangare ne na bukukuwan cika shekaru biyu na mulkin gwamnatin Biodun.
A wajen taron, an karrama ma’aikata 82 ta hanyar ba su lambar yabo da kuma kyautar kudi da ta kai Naira miliyan 42 sakamakon yin nuna hazaka a fannoni daban-daban.
Gwamnan wanda da kan sa ya gabatar da kudin ga wasu daga cikin wadanda aka karrama, ya yaba da sadaukarwar da ma’aikatan jihar suka yi duk da kalubalen da suka fuskanta.
Gwamna ya magantu kan sabon albashi
Wani rahoto da shafin yanar gizon gwamnatin Ekiti ya fitar, ya rahoto Biodun ya ba ma'ikatan jihar tabbacin cewa nan ba da dadewa ba za su fara samun sabon mafi karancin albashi.
Oyebanji ya nemi ma’aikata da su aminta da shugabannin kungiyoyinsu yayin da suke tattaunawa kan yadda za a aiwatar da sabon albashi.
“Ba domin goyon bayanku ba, da ba mu cimma wannan muhimmin aikin da muka yi ba. Tsare tsaren gwamnati za su yi tasiri ne idan an samu hazikan ma'aikata kamar ku."
- Gwamnan Biodun Oyebanji
Gwamna ya daina biyan mafi karancin albashi
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Ekiti ta dakatar da biyan mafi karancin albashi, sannan ta zabtare albashin ma'aikata da hadiman gwamna.
Wannan na zuwa ne yayin da aka cimma wata yarjejeniya tsakanin gwamnatin jihar da kungiyoyin kwadago amma dakatarwar ba ta shafi kananun ma'aikata ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng