Gwamna Ya Dakatar da Biyan Mafi Ƙarancin Albashi, Ya Zabtare Albashin Ma’aikatan Jiharsa
- Gwamnatin jihar Ekiti ƙarƙashin jagorancin Kayode Fayemi, ta dakatar da biyan mafi ƙarancin albashi ga wani rukunin ma'aikatan jihar
- Wanna na ƙunshe ne a wata yarjejeniya da aka cimma wa tsakanin gwamnatin da ƙungiyoyin ƙwadugo na jihar
- Daga cikin yarjejeniyar akwai zabtare kashi 25% na albashin hadiman gwamnati
Gwamnatin jihar Ekiti, ranar Jumu'a, ta dakatar da biyan mafi ƙarancin albashi na N30,000, sannan ta zabtare albashin ma'aikata da hadiman gwamnatin jihar, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Najeriya Zata Samar Da Manyan Wayoyin Hannu Ga Ƙasashen Africa, Pantami
Ma'aikatan jihar dake mataki na 07 zuwa 12 sun fara cin gajiyar mafi ƙarancin albashi tun watan Janairun wannan shekarar, amma a yanzun an dakatar dashi na tsawon watanni uku.
The cable ta ruwaito cewa, ma'aikatan dake mataki na 01 zuwa 06 sun taki sa'a domin su ba'a taɓa musu albashin su ba.
A watan Disamba 2020, ƙungiyar ƙwadigo ta jihar tayi barazanar tsayar da komai na jihar matuƙar gwamna Kayode Fayemi yaƙi fara biyan mafi ƙarancin albashi na N30,000.
Legit.ng hausa ta gano cewa a watan Maris, an samu wani lokaci da komai ya tsaya cak a majalisar dokokin jihar saboda zanga-zangar lumana da ma'aikata suka yi kan mafi ƙarancin albashi.
Zabtare albashin da gwamnati tayi, yana daga cikin yarjejeniyar da akayi ranar jumu'a a Ado-Ekiti, babban birnin jihar, wadda gwamnati da ƙungiyar kwadugo suka sanya hannu.
KARANTA ANAN: Karin Bayani: Gwamnan Cross Rivers Ya Gana da Buhari a Karon Farko Bayan Komawarsa APC
Daga cikin abubuwan da yarjejeniyar ta ƙunsa kamar yadda shugaban ƙungiyar yan kasuwa na jihar (TUC), Sola Adigun, ya karanta yace: "An dakatar da biyan mafi ƙarancin albashi ga wani rukuni na ma'aikata na tsawon watan Mayu Zuwa Yuli."
Hakanan kuma an amince da zabtare kashi 25% daga cikin albashin hadiman gwamnatin jihar.
A wani labarin Kuma Babbar Magana: PDP Ta Buƙaci Wani Gwamna Yayi Murabus Daga Muƙaminsa
Jam'iyyar hamayya ta PDP reshen jihar Imo tayi kira ga gwamnan jihar yayi murabus daga kujerarsa, kamar yadda punch ta ruwaito.
PDP tace gwamnan bashi da karsashi ko ƙwarin guiwar da zai fuskanci matsalar tsaron da take kara yawaita a jihar.
Asali: Legit.ng