Sojoji Sun Samu Gagarumar Nasara, An Kashe Hatsabiban 'Yan Bindiga a Arewa

Sojoji Sun Samu Gagarumar Nasara, An Kashe Hatsabiban 'Yan Bindiga a Arewa

  • Dakarun sojojin Najeriya sun kaddamar da farmaki kan wasu gungun 'yan bindiga a kauyen Maraban Kyaware da ke jihar Zamfara
  • An rahoto cewa sojojin sun kai farmakin ne da sanyin safiyar Laraba bayan samun bayanan sirri da suka kai su ga samun nasara
  • Rahoto ya nuna sojojin sun kashe hatsabiban 'yan bindiga biyar tare da jikkata wasu da dama lamarin da ya sa sauran tserewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - Rundunar sojojin Najeriya sun sake samun gagagarumar nasara a kokarin da suke yi na kakkabe 'yan ta'adda a Arewa maso Yamma.

Dakarun sojin da ke atisayen Hadarin Daji a jihar Zamfara sun kashe hatsabiban 'yan bindiga biyar a wani artabu da suka yi a safiyar ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi wa jama'a barazana, sun sha alwashin kai hari Zamfara

Sojoji sun kakkabe 'yan bindiga a jihar Zamfara
Sojoji sun halaka 'yan ta'adda 5 a samamen da suka kai jihar Zamfara. Hoto: Audu Marte
Asali: Getty Images

Dakarun Sojoji sun kakkabe 'yan bindiga 5

Mai sharhi kan harkokin 'yan ta'adda a yankin Tafkin Chadi, Zagola Makama ne ya bayyana hakan a shafinsa na X a ranar 16 ga Oktoba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton Makama ya nuna cewa dakarun sojojin sun kashe 'yan ta'adda biyar a karan battar da suka yi a kauyen Maraban Kyaware da ke karamar hukumar Tsafe.

An ce arangamar ta yi sanadiyyar samun raunuka a jikin 'yan bindiga da dama yayin da sojojin suka kai samame kan 'yan ta'addan a safiyar Laraba.

Sojoji sun tilastawa 'yan bindiga tserewa

Majiyar ta bayyana cewa:

"Dakarun sojojin Najeriya na Hadarin Daji sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga biyar a wani artabu da suka yi a Mararaban Kyaware da ke karamar hukumar Tsafe.
"Wannan arangamar da ta faru da sanyin safiyar Larabar nan, yayin wani samamen da sojoji suka kai, ya kuma yi sanadiyyar jikkata wasu ‘yan bindiga da dama.

Kara karanta wannan

An yi artabu tsakanin bangarori 2 na yan bindiga da suka farmaki sakatariyar APC

Dakarun da suka kai samamen bayan samun bayanan sirri sun yi artabu da ‘yan bindigar, inda suka yi galaba a kansu tare da tilastawa sauran maharan tserewa."

'Yan bindiga sun yi wa jama'a barazana

A wani labarin, mun ruwaito cewa mazauna karamar hukumar Anka, jihar Zamfara sun nemi daukin gwamnati da jami'an tsaro kan barazanar da 'yan bindiga suka yi masu.

An ce wata dabar 'yan bindiga ce ta aika sakon gargadi ga mazauna Anka, ta ce za ta kai masu hare-hare a gonakinsu da sauran sassan karamar hukumar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.