Mafi Karancin Albashi: Jerin Gwamnonin da Za Su Biya Ma'aikata Fiye da N70000

Mafi Karancin Albashi: Jerin Gwamnonin da Za Su Biya Ma'aikata Fiye da N70000

  • An dade ana tafka muhawara kan batun mafi karancin albashi tun bayan da Shugaba Bola Tinubu ya janye tallafin man fetur
  • Kungiyar kwadago ta kwashe watanni tana tattaunawa da gwamnatin tarayya kafin amince da sabon albashin N70,000 ga ma'aikata
  • Sai dai wasu gwamnoni sun sanar da cewa za su biya albashin da ya zarce wanda gwamnati da 'yan kwadago suka amince da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Fafutukar neman sabon mafi karancin albashi ya fara ne daga ranar da Shugaban Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur a kasar nan.

Bayan shafe watanni ana tattaunawa tsakanin shugabannin kwadago da gwamnatin tarayya, an amince da N70,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya gwangwaje hazikan ma'aikata 82 da Naira miliyan kyautar N42m

Gombe, Ogun da wasu jihohi biyu sun sanar da biyan albashin sama da N70,000
Gwamnonin Najeriya da ke biyan mafi karancin albashi fiye da na gwamnatin tarayya. Hoto: @Safiyanudm, @DapoAbiodunCON, @OndoAPC
Asali: Twitter

Gwamnonin da za su biya sama da N70,000

Wannan karin kudin ya shafi duk ma'aikatun da ke da ma'aikata akalla 50, kuma an yi hakan da nufin inganta rayuwar miliyoyin ma'aikata da kuma rage talauci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

To sai dai kuma, akwai wasu gwamnonin sun sanar da fara biyan sama da N70,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikata a jihohinsu.

A ƙasa akwai jerin gwamnonin da suka yi irin wannan sanarwar kwanan nan kamar yadda Legit.ng ta tattaro:

1. Gwamna Yahaya na Gombe

Kungiyar kwadago ta NLC da Gwamna Muhammad Yahaya na jihar Gombe sun cimma yarjejeniyar aiwatar da sabon mafi karancin albashi na N71,451, inji rahoton Daily Trust.

An cimma wannan matsayar ne yayin da ake rade radin cewa jihar ba za ta iya biyan albashin N70,000 da gwamnatin tarayya ta amince da shi da shugabannin kwadago ba.

Kara karanta wannan

Rikicin jam'iyya: An bayyana lokacin da Damagum zai sauka daga shugaban PDP

2. Gwamna Abiodun zai biya albashin N77,000

A kwanakin baya ne gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya sanar da amincewa da N77,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma’aikata a jihar.

Bayan ganawa da shugabannin kungiyar kwadago, gwamnan ya bayyana cewa sabon mafi karancin albashin zai fara aiki nan take.

3. Gwamnatin Ondo za ta biya N73,000

Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya sanar da fara aiwatar da N73,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma’aikata a jihar.

Aiyedatiwa, dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar Ondo da za a yi a ranar 16 ga watan Nuwamba, ya bayyana ci gaban a wurin yakin neman zabensa.

Ya kuma jaddada cewa gwamnatin jihar na biyan albashin ma’aikata akai-akai tare da bayar da horo da kuma karin girma.

4. Ododo zai biya N72,500 ga ma’aikata

Gwamna Ahmed Ododo na jihar Kogi ya na cikin gwamnonin da suka amince da biyan sabon mafi karancin albashi, inda zai rika biyan N72,500.

Kara karanta wannan

Gwamna a Arewa ya zabtare 55% a farashin shinkafa da wasu kayan abinci

Matakin Gwamna Ododo ya biyo bayan gabatar da rahoton kwamitin mafi karancin albashi a ranar Litinin, 7 ga watan Oktoba.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa za a fara biyan sabon mafi karancin albashin da aka amince da shi a watan Oktoba.

An yi watsi da albashin N70,000

A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar yan fansho a Kudu maso Yammacin Najeriya ta ce gwamnatin tarayya ta yi wa 'yan kwadago wayo kan mafi karancin albashi.

Kakakin kungiyar NUP, Dakta Olusegun Abatan ya ce dole a sake zama kan albashi tun da gwamnatin tarayya ta kara kudin fetur inda ya nemi a mayar da albashin zuwa N250,000.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.