Gwamnati Ta Bayyana Halin da Ake Ciki bayan Durkushewar Tashar Wutar Lantarki
- Gwamnatin tarayya ta ce ana ci gaba da aikin gyara tashar wutar lantarkin kasar da ta lalace a ranar Litinin, 14 ga watan Oktoba
- A cikin wata sanarwa a 15 ga Oktoba, TCN ya bayyana cewa tashar samar da lantarkin ta durkushe ne a yammacin ranar Litinin
- Legit Hausa ta ruwaito cewa HURIWA ta nemi Shugaba Bola Tinubu da ya kori ministan makamashi saboda lalacewar wutar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – A ranar 15 ga watan Oktoba ne kamfanin wutar lantarkin Najeriya (TCN) ya sanar da cewa an kusa kammala gyara tashar lantarkin kasar da ta lalace.
Tabbacin da kamfanin TCN ya bayar ya biyo bayan durkushewar da babbar tashar wutar lantarkin kasar ta yi a karo na biyu a cikin awanni 24.
TCN na kokarin gyara tashar wutar lantarki
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, manajan hulda da jama’a na TCN, Ndidi Mbah, ya ce an kusa kammala gyaran tashar wutar lantarkin, a cewar rahoton Channels.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce tuni aka fara gyara tashar wutar lantarkin kuma tashar wutar lantarki ta Azura na ba da gudunmawa zuwa lokacin da za a kammala gyaran.
Kamfanin ya ce da karfe 10:24 na safiyar Talata, "an cimma babbar nasara a yunkurin farfado da tashar wutar amma sai aka sake cin karo da wani kalubalen da ya haifar da koma baya".
Wuraren da suka samu wutar lantarki
Jaridar ThisDay ta rahoto cewa TCN ya ce an maido da wutar lantarki a wasu yankuna na Abuja da wasu manyan cibiyoyin rarraba wutar da ke sassan kasar.
A cewar sanarwar da Mbah ta fitar, durkushewar tashar ba ta shafi cibiyar samar da iskar gas ta Ibom ba. Ta ce cibiyar na samar da lantarki ga yankin Kudu maso Kudu.
Mbah ta ce za a gudanar da bincike kan musabbabin faruwar lamarin da zaran an kammala gyara babbar tashar lantarkin gaba daya.
HURIWA ta nemi a kori Ministan makamashi
A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar marubutan kare hakkokin dan Adam ta Najeriya (HURIWA) ta nuna damuwa kan durkushewar tashar wutar lantarkin kasar nan.
HURIWA ta nemi shugaba Bola Tinubu da ya sallami ministan makamashi, Adebayo Adelabu wanda ta ce ba ya aikin komai kan wutar lantarkin a matsayinsa na minista.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng