An Fadawa Tinubu Ministan da Zai Kora Yayin da 'Yan Najeriya Ke Kwana a Duhu

An Fadawa Tinubu Ministan da Zai Kora Yayin da 'Yan Najeriya Ke Kwana a Duhu

  • Kungiyar HURIWA mai fafutukar kare hakkin al'umma ta ce ministan makamashi, "ba ya yin wani aikin a zo a gani"
  • A yayin da babbar tashar wutar lantarki ta sake lalacewa, HURIWA ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya sallami Adebayo Adelabu
  • Legit Hausa ta rahoto cewa 'yan Najeriya sun shiga cikin duhu bayan tashar lantarkin ta lalace karo na biyu a cikin awowi 24

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Kungiyar marubutan kare hakkokin dan Adam ta Najeriya (HURIWA) ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya gaggauta korar ministan makamashi, Adebayo Adelabu.

HURIWA ta nuna rashin gamsuwa da kuma bacin ranta dangane da yawan lalacewar babbar tashar wutar lantarki ta kasa a karkashin gwamnatin Tinubu.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta bayyana halin da ake ciki bayan durkushewar tashar wutar lantarki

HURIWA ta yi magana kan durkushewar tashar wutar lantarki
HURIWA ta nemi Tinubu ya sallami ministan makamashi. Hoto: @PBATMediaCentre
Asali: Facebook

'Minista ba ya yin aikin komai' - HURIWA

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Emmanuel Onwubiko, kodinetan kungiyar na kasa ya fitar, wadda Legit.ng ta samu a ranar Talata, 15 ga watan Oktoba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamared Onwubiko ya soki Tinubu kan nada dan siyasar da ba shi da masaniya kan sarrafa wutar lantarki, inda ya ce wutar lantarki ce kashin bayan ci gaban tattalin Najeriya.

HURIWA ta ce:

“Mun gaza fahimtar dalilin da ya sa Tinubu ke ganin akwai amfani a bar mutum kamarsa (ya na nufin Adelabu) wanda ba ya yin aikin komai a matsayin ministan makamashi.
"Yin irin wannan nadin shi ne babban kuskuren da gwamnatin Najeriya ta yi, wanda kuma ya kamata a gaggauta yin sauyin da zai kawo karshen matsalar."

HURIWA ta caccaki tsofaffin ministoci

Kungiyar ta ce ma’aikatar wutar lantarki ta kasance gida ga 'yan siyasar da ba sa tabuka abin kirki, kuma zaman Adelabu matsayin minista bai sauya komai ba.

Kara karanta wannan

Cikakken jerin gwamnonin CBN daga 1958 zuwa yau da manyan nasarorin da suka samu

Jaridar Daily Post ta rahoto HURIWA na cewa:

"Najeriya dai ta gamu da rashin sa a bangaren ministocin da ake nadawa ma'aikatar nmakamashi a cikin shekaru ashirin.
"Da yawan wadanda aka nada suna fadawa komar hukumomin yaki da rashawa kuma har su bar ofis ba sa tabuka komai game da matsalolin wutar lantarkin kasar."

Tashar wutar lantarki ta lalace

A wani labarin, mun ruwaito cewa babbar tashar wutar lantarki ta durkushe a ranar Talata, 15 ga watan Oktoba wanda ya kai ga katsewar wutar lantarki a fadin kasar.

Kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) sun sanar da dakatar da aikin rarraba wutar a wata sanarwa daban-daban a ranar Talata, 15 ga watan Oktoba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.