T Pain da Sauran Sunaye 4 da Aka Lakawa Tinubu da Dalilan Alakanta Shi da Su
Shugaban kasar Najeriya na 16, Bola Ahmed Tinubu ya samu sunayen inkiya kala-kala a rayuwarsa tun kafin ya zama shugaba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Sunayen sun samo asali ne daga yabo ko sukarsa musamman yanayin mulkinsa da kuma lankaya masa su saboda burgewa da ya yi.
Sunayen da aka radawa Bola Tinubu
The Guardian ta ruwaito cewa akalla akwai sunayen inkiya guda biyar da aka lakawa Tinubu tun kafin zama shugaban kasar Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta yi duba game da sunayen tare da bincikar musabbabin radawa shugaban kasar.
1. Jagaban
An samu wannan kalmar daga yaren Hausa wanda ke nufin mai jagorantar al'umma.
Magoya bayan Bola Tinubu ne suka laka masa sunan saboda yadda yake da karfi a yankinsa musamman ta bangaren siyasa.
Asalin sunan, 'Jagaban Borgu' na nufin jarumi da ke jagorantar yaki da marigayi Sarkin Borgu, Halliru Dantoro Kitoro III ya nada shi a 2006.
2. Asiwaju
Wannan inkiya na da kusan ma'ana guda daya da 'Jagaban' wanda ke nufin wanda zai yi jagora ko mai jagora.
Asiwaju kalma ce ta Yarbanci da ke nuni da fikira da mutum ke da shi a siyasa da ke sauya akalar abubuwa kamar yadda Bola Tinubu yake.
3. City Boy
Wannar kalma ce ta Turanci da ke nufin dan birni da aka lakawa Bola Tinubu tuntuni, Sahara Reporters ta ruwaito.
Hakan bai rasa nasaba da yadda ya yi gwagwarmaya a birni kamar Lagos kuma ya zama kan gaba musamman a siyasa.
4. Emilokan
Wannan inkiya ya faro ne lokacin da Bola Tinubu ke neman shugabancin Najeriya ido a rufe.
Emilokan kalmar Yarbanci ce da ke nufin 'lokaci na ne' da aka yi ta yadawa bayan Tinubu ya furta hakan gabannin kamfen zaben 2023.
5. T-Pain
A kwanakin nan aka lakawa Bola Tinubu wannan suna da ke nuna halin kunci da ake ciki, cewar TheCable.
'T' na nufin Tinubu kenan sai kuma 'Pain' da ake nufi a Hausa da kunci ko kuma zafi wanda ke nufin irin halin da al'umma ke ciki a mulkin Tinubu.
Duk da T-Pain sunan wani mawaki ne a Amurka, amma magoya bayan Tinubu sun sauya masa ma'ana.
Sun bayyana cewa 'T-Pain da 'Temporary Pain' a matsayin wahala na lokaci kadan, watau duk wahalar da ake ciki zai wuce nan ba da jimawa ba.
Tinubu ya ba da tabbacin kawo sauki
Mun ba ku labarin cewa shugaba Bola Tinubu ya yi magana kan halin kunci da yan Najeriya ke fama da shi a kasar.
Tinubu ya ce da shi da mataimakinsa, Kashim Shettima suna jin tausayi a zuciyarsu kan halin da al'umma ke ciki a yanzu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng