Kano: Za a Sake Gina Cibiyar Bunkasa Fasaha da Aka Lalata Lokacin Zanga Zanga

Kano: Za a Sake Gina Cibiyar Bunkasa Fasaha da Aka Lalata Lokacin Zanga Zanga

  • Gwamnatin Kano ta bayyana bacin rai kan yadda mazu zanga zanga su ka lalata cibiyar bunckasa fasahar zamani
  • Mataimakin gwamna, Aminu AbdulSalam Gwarzo ya ce lamarin ya jawo koma baya ga cigaban fasaha a jihar da kasa baki daya
  • Ya tabbatarwa tawagar gwamnatin tarayya cewa jami'an tsaro sun yi nasarar kwato wasu daga cikin kayan cibiyar da aka sace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Gwamnatin Kano ta ce za ta sa ke gina cibiyar bunkasa fasahar zamani ta 'Digital Industrial Park' da aka lalata a lokacin zanga zanga a jihar.

Masu zanga zangar #EndBadGovernance da aka fara a ranar 1 ga Agusta, 2024 ne su ka lalata cibiyar, tare da lalata kayan kayan biliyoyi da gwamnatin tarayya ta zuba a ciki.

Kara karanta wannan

"A kasa su ke zaune:" Gwamna ya koma makarantar mata a Kano da kayan aiki

Abba Kabir
Gwamnatin Kano za ta gyara cibiyar fasaha Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo ne ya bayyana cewa za a yi gyaran a ziyarar da Ministan Sadarwa, Dakta Bosun Tijjani ya kawo Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta yi tir da lalata cibiyar fasaha

Ibrahim Garba Shu'aibu ya tabbatarwa Legit cewa mataimakin gwamnan Kano, Aminu AbdulSalam ya yi Allah wadai da lalata cibiyar fasaha a jihar.

Ya bayyana barnar da masu zanga-zangar su ka yi a matsayin babbar koma baya ga ci gaban fasahar sadarwa da muradun fasaha a Kano da kasa baki daya.

Gwamnatin Kano za ta gyara cibiyar fasaha

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa za ta yi aikin gara cibiyar fasaha da masu zanga zanga su ka lalata a jihar Kano, tare da tabbatar da cewa an soma kokarin dawo da wurin yadda ya ke.

Kara karanta wannan

Gobara: Gwamna ya cika alkawari, Abba ya ba yan kasuwa tallafin N100m

Mataimakin gwamnan Kano, Aminu AbdulSalam Gwarzo ya ce hukumomin tsaro tare da taimakon shugabannin al’umma sun yi nasarar kwato mafi yawan kayan aikin da aka sace.

Ana son dauke cibiyar fasaha daga Kano

A wani labarin kun ji cewa majalisar matasan Arewa ta ki amincewa da bukatun wasu mutane da cewa a dauke cibiyar fasaha daga Kano bayan masu zanga zanga sun yi mata fata-fata.

A sanarwar da shugaban majalisar, Dr. Aliyu Mohammed da sakatarensa, Hafiz Garba su ka fitar, sun ce duk da matasan da su ka lalata cibiyar ba su kyauta ba, amma bai dace a nemi dauke ta daga Kano ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.