Yan Sanda Sun Farauto Gawurtattun Yan Fashi da Makami

Yan Sanda Sun Farauto Gawurtattun Yan Fashi da Makami

  • Rundunar yan sanda a jihar Jigawa ta cafke wasu fitinannun yan fashi da ke bin jama'a su na yi masu kwace
  • Matasan da aka kama na gudanar da ayyukansu a wasu kebantattun unguwanni da ke jihar, har da gidan dan siyasa
  • Rundunar ta sha alwashin tabbatar da cewa matasan sun dandana kudarsa bayan an gurfanar da su a gaban kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa

Jihar Jigawa - Rundunar yan sanda reshen Jigawa ta samu nasarar cafke wasu daga cikin mugayen yan fashi da makami da su ka addabi yankin.

Rundunar yan sandan jihar ta bayyana cewa yan fashi da makamin sun ware wasu yankuna inda su ka fi kai wa farmaki.

Kara karanta wannan

Yan fashi sun mamaye unguwa tsakar dare, sun bi gida gida suna ta'addanci

Police
An kama yan fashi a Jigawa Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Tashar TVC News ta wallafa cewa an kama matasan yan fashi, inda ake zarginsu da fashi da makami a sassa daban daban na Jigawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ina yan fashi su ka kai hari?

Rundunar yan sandan jihar Jigawa ta bayyana cewa matasan da ta kama bisa zargin fashi da makami sun ware wuraren da su ka fi zuwa mugun aikinsu.

Daga cikin wuraren da su ka yi wa fashi akwai unguwar Gida dubu, gidan wani fitaccen dan siyasa da aka boye sunansa, otal da yankin Galanawa da 'Highbrow.'

Wani mataki za a dauka kan 'yan fashin?

Rundunar yan sanda Jigawa ta ce mutanen da aka kama da zargin fashi da makami na hannunsu, ana zurfafa bincike kan salon abin da su ka aikata.

Rundunar ta bayyana cewa da zarar bincike ga kammala, za a tesa keyar matasan gaban kotun domin a yanke masu hukunci dai-dai da laifinsu.

Kara karanta wannan

An harbe shugaban yan sanda da wasu jami'ai yayin artabu da yan bindiga

An kama tarin yan fashi a Jigawa

A baya mun wallafa cewa rundunar yan sandan Jigawa ta kama yan fashi da makami masu tarin yawa da ke kwace kayan jama'a a kananan hukumomin jihar.

Daga cikin kananan hukumomin da yan fashin ke takurawa akwai Gwaram, Hadejia, Malam Madori, Kazaure, Dutse da Gwiwa, kuma tuni bincike ya yi zurfi a kansu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.