An Harbe Shugaban Yan Sanda da Wasu Jami’ai yayin Artabu da Yan Bindiga

An Harbe Shugaban Yan Sanda da Wasu Jami’ai yayin Artabu da Yan Bindiga

  • Rahotanni da suka fito daga jihar Delta na nuni da cewa wata tawagar yan sanda ta hadu ba babban tsautsayi yayin artabu da miyagu
  • A yayin artabun, yan bindiga sun harbe shugaban yan sandar da yake jagorantar rundunar yayin da wasu suka samu raunuka
  • Rundunar yan sandan jihar Delta ta tabbatar da faruwar lamarin kuma ta ce abin ya faru ne a safiyar yau Litinin, 14 ga watan Oktoba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Delta - Rundunar yan sanda ta yi babban rashi yayin da yan bindiga suka harbe mata babban jami'i.

Lamarin ya faru ne a safiyar yau Litinin yayin da yan sanda suka tunkari wata moɓoyar yan bindiga domin ceto mutane.

Kara karanta wannan

Yan daba sun harbi shahararren ɗan TikTok, sun sace masa gwala gwalai

Yan sanda
An kashe babban dan sanda a Delta. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa kakakin yan sandan jihar Delta, SP Bright Edafe ya tabbatar da faruwar lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An harbe shugaban yan sanda a Delta

Rahotanni na nuni da cewa yan bindiga sun harbe ɗan sanda mai matsayin DPO da ya jagoranci runduna domin kai farmaki.

Punch ta wallafa cewa kakakin yan sanda jihar Delta ya ce rundunar ba za ta bayyana sunan jami'in da ya rasu ba saboda girmama shi.

An jikkata wasu yan sanda a Delta

Wani mai rajin kare hakkin dan Adam, Kwamared Israel Joe ya ce bayan babban dan sandar, an kashe wasu jami'ai da dama.

Haka zalika rundunar yan sanda ta tabbatar da cewa wani jami'i na DPO yana kwance a asibiti saboda rauni da ya samu yayin artabun.

Yan banda sun shiga neman yan bindiga

Biyo bayan faruwar lamarin, an ruwaito cewa yan bangar yankin sun shiga jeji domin gano miyagun.

Kara karanta wannan

An ceto mutane wajen yan bindigar da suka ƙona dan sanda a kasuwa

Wata majiya ta tabbatar da cewa jami'in da aka kashe bai wuce kwana biyu da fara aiki a ofishin yan sandan da aka turo shi ba.

An ba sojoji umarni kan yan bindiga

A wani rahoton, kun ji cewa sojoji sun yi kira na musamman ga sojoji kan tunkarar yan bindiga da sauran miyagu masu tayar da fitina.

Manjo Janar Kelvin Aligbe ne ya sake yi wa sojojin caji a wani taron jarrabawar karin matsayi da aka yi wa sojojin Najeriya a jihar Ondo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng