Ana Kokarin Shawo kan Tsadar Fetur, Farashin Gas Din Girki Ya Lula Sama

Ana Kokarin Shawo kan Tsadar Fetur, Farashin Gas Din Girki Ya Lula Sama

  • An samu karuwar farashin gas din girki a wasu daga cikin jihohin kasar nan, inda kowane kilo ya kai N1,500 a wasu wuraren
  • Zuwa yanzu dai, an samu rahoton karuwar farashin a wasu daga cikin jihohin Kudancin kasar nan har da babban birnin tarayya
  • Sai dai an dora alhakin tsadar da aka samu a yanzu kan yadda ake dauko sama da 60% ma gas din girki daga kasashen waje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos - A daidai lokacin da yan kasar nan ke kokawa da karin farashin fetur, yanzu haka an samu karin farashin gas din girki a wasu jihohin.

Kara karanta wannan

'A fita zanga zanga,' Yadda aka yi rubdugu ga Tinubu kan tashin kudin fetur

Wuraren da aka samu karuwar farashin gas din sun hada da Abuja, Legas da Ogun, inda lamarin ya fi kamari a babban birnin tarayya.

Iskar gas
Farashin gas ya tashi a wasu sassan Najeriya Hoto: Aleksandar Georgiev
Asali: Getty Images

Jaridar Punch ta tattaro cewa a danganta tsadar da gas din ga yi saboda ana dauko shi daga kasashen waje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wuraren da farashin gas ya tashi

A jihohin Legas da Ogun, ana sayar da kowane kilo da gas a kan N1,500 lamarin da ke nuna cewa kowane kilo 12.5 ya kusa N19,000. A babban birnin tarayya Abuja kuwa, an samu karin farashin gas da 41.6%, inda ake sayar da kowane kilo 12.5 a kan N17,000.

Ana sa ran farashin gas ya sauko

Manajan Daraktan NIPCO Pls, Suresh Kumar ya bayyana cewa matatar Dangote da sauran matatun cikin gida za su iya sauko da farashin gas a fadin kasar nan.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Majalisa ta yi albishir ga yan kasa kan saukar farashin fetur

Ya bayyana damuwa kan yadda ake shigo da sama da 60% na gas din da ake girki da shi daga kasashen ketare.

Farashin gas din girki ya sake hawa

A wani labarin kun ji cewa an kara samun hauhawar farashin gas din girki wanda ya ke neman kai wa N2,000 inda masu dillancinsa a kasar nan su ka ce da tsada su ke saro shi.

Tsadar farashin gas din girki ya fara sanya wasu daga mazauna kasar nan sauya tunani, inda tuni wasu su ka koma amfani da gawayi a wajen girki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.