'Duk Inda Kuka ga Abinci Ku ci, Akpabio ya ba Yan Kasa Shawara a Bidiyo, an Soke Shi
- Yayin da ake tsaka da wahalar tsadar rayuwa a Najeriya, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya ba da shawara
- Akpabio ya ba yan kasar shawara wanda ya jawo cece-kuce inda yan Najeriya suka caccake shi da cewa yana musu isgilanci
- Hakan ya biyo bayan baram-barama da Akpabio ya yi a bidiyo da yake ba yan kasar shawara kada su yi wasa da duk inda suka abinci su ci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya yi magana kan halin kunci da ake ciki.
Akpabio ya shawarci yan Najeriya da su yi amfani da damar su suka samu lokacin da suka ga abincin kyauta.
Akpabio ya sake jawo cece-kuce a Najeriya
Shugaban Majalisar ya fadi haka ne a cikin wani faifan bidiyo da Tribune ta wallafa a yau Lahadi 13 ga watan Oktoban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Maganar Akpabio ta jawo cece-kuce ganin cewa ya yi ta a daidai lokacin da yan kasar ke cikin halin kunci.
Akpabio ya ba da shawarar ce duba da yadda abinci ya yi tsada a wannan lokaci da ake ciki.
Yan Najeriya sun caccaki Godswill Akpabio
Ya ce kada yan Najeriya su yi wasa da duk wani abincin kyauta da suka gani a wadace saboda halin da ake ciki.
Wannan ba shi ne karon farko da Akpabio ke katobara da ke cin karo da ra'ayin yan Najeriya ba wanda suka caccake shi.
A watan Yulin 2024, Akpabio ya fada a wani taro cewa mambobin Majalisa za su yi ta cin abinci yayin da matasa ke kan tituna suna zanga-zanga.
Akpabio ya nemi alfarmar yan Najeriya
Kun ji cewa Majalisar Dattawan Najeriya ta buƙaci masu shirya zanga-zanga a faɗin ƙasar nan su kai zuciya nesa.
Shugaban majalisar dattawan, Sanata Godswill Akpabio, wanda ya yi roƙon ya buƙace su da haƙura da gudanar da zanga-zangar.
Ya bayyana cewa gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta kawo shirye-shiryen da za su amfani ƴan Najeriya nan gaba kaɗan.
Asali: Legit.ng