Kotu Ta Yi Hukunci kan Zargin Hon. Doguwa da Kisan Kai, an Ci Tarar Abba Kabir
- Yayin da ake zargin Hon. Alhassan Ado Doguwa da kisan kai tun zaben 2023, Kotun Daukaka Kara ta wanke shi
- Kotun karkashin jagorancin Mai Shari'a, Donatus Okorowo ya yi fatali da korafin gwamnatin jihar Kano kan doguwa
- Alkalin ya kuma umarci gwamnatin jihar ta guji kamawa da tsarewa ko hukunta Doguwa inda ya ci tararta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kotun Daukaka Kara ta yi hukunci kan zargin Hon. Alhassan Ado Doguwa da kisan kai a zaben 2023.
Kotun ta tabbatar da wanke dan Majalisar daga jihar Kano inda ta haramtawa Abba Kabir kama shi da kuma cin zarafinsa.
Zargin kisan kai: Kotu ta wanke Hon. Doguwa
Alkalin kotun, Mai Shari'a, Donatus Okorowo shi ya yanke hukuncin inda ya umarci biyan Doguwa diyyar kudi har N25m, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun ta yi fatali da korafin gwamnatin jihar Kano kan shigar da Hon. Doguwa kara da zargin kisan kai a zaben 2023.
Hon. Doguwa ya ce korafin da aka shigar game da shi kan rigimar zaben 2023 an yi bincike kuma yan sanda da babbar kotun jihar Kano sun wanke shi.
Hon. Doguwa ya yi godiya ga Ubangiji
Da ya ke martani kan hukuncin kotun, Hon. Doguwa ya yi godiya ga Ubangiji tare da nuna kwarin guiwa a bangaren shari'a a Najeriya, Thisday ta ruwaito.
"Mun godewa Allah da ya sake tabbatar da gaskiyarmu da kuma kare mu daga sharrin makiya yan adawa."
"Ina kira ga magoya bayana da su yi murnar wurin godewa Allah game da nasarar da muka samu da kaucewa take doka da oda."
- Hon. Alhassan Ado Doguwa
2027: Doguwa ya caccaki Sanata Rabiu Kwankwaso
Kun ji cewa dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar Tudun Wada/Doguwa a Kano ya mayarwa Rabiu Musa Kwankwaso martani.
Hon. Alhassan Doguwa ya ce har yanzu Kwankwaso a kidime yake bayan faduwa zaben 2023 a hannun Bola Tinubu.
Doguwa ya shawarci Kwankwaso ya mayar da hankali kan zaben 2027 inda za a yi masa ritaya gaba daya a siyasa.
Asali: Legit.ng