Ana Jita Jitar Rashin Lafiyar Tinubu, Hadiminsa Ya Fadi Halin da Ya Ke ciki

Ana Jita Jitar Rashin Lafiyar Tinubu, Hadiminsa Ya Fadi Halin da Ya Ke ciki

  • Hadimin Shugaba Bola Tinubu a bangaren siyasa, Ibrahim Masari ya yi magana kan rade-radin rashin lafiyar shugaban
  • Masari ya yi fatali da jita-jitar inda ya ce Tinubu lafiyarsa kalau kuma yana cikin koshin lafiya a inda ya ke hutu
  • Hadimin ya shawarci masu yada jita-jitar da su yi hakuri da lafiya da rashinta duka na hannun Ubangiji mahalicci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - An samu karin bayani kan jita-jitar da ake yi cewa Bola Tinubu ba shi da lafiya yana karbar kulawa a ketare.

Hadimin Tinubu a bangaren siyasa, Ibrahim Masari ya fadi halin da shugaban ke ciki a yanzu bayan kai masa ziyara.

Kara karanta wannan

An samu mutumin farko da aka gani da Tinubu a Ingila, ya fadi halin da ake ciki

Bayanai sun fito kan rade-radin rashin lafiyar Bola Tinubu
Hadimin Bola Tinubu ya yi magana kan jita-jitar da ake yadawa kan rashin lafiyar Bola Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Hadimin Tinubu ya kore jita-jitar rashin lafiya

Masari ya bayyana haka ne yayin hira da DCL Hausa da ta wallafa a shafin Facebook a yau Asabar 12 ga watan Oktoban 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masari ya kore jita-jitar da ake yadawa kan cewa shugaban yana cikin wani irin hali na rashin lafiya.

Hakan ya biyo bayan zargin cewa shugaban kasar ba shi da lafiya da har wasu me yin masa mummunan fata.

Halin da Tinubu ke ciki kan rashin lafiya

"Duk wanda kake yi wa fatan mutuwa kamar kana kara masa nisan kwana ne."
"Wadanda ke cewa Alhaji Bala Ashiru Tanimu ga su ga Allah nan wanda ke da rayuwa da lafiya da rashin lafiya."
"Ina tabbatar maka da cewa Allah ya albarkace shi da lafiya kuma in sha Allah zai dawo gida ba tare da bata lokaci idan hutunsa ya kare."

Kara karanta wannan

'Ba laifinsa ba ne', Ndume ya fadi nufin Tinubu, ya roki alfarma bayan tsadar fetur

- Ibrahim Masari

Masari ya ce babu wani maganar ganin likita da ake yaɗawa cewa Tinubu ya je yi a birnin Landan.

Masari ya gana da Tinubu a ketare

A baya, kun ji cewa Ibrahim Kabir Masari ya yi zama da Bola Ahmed Tinubu a gidansa da ke Birtaniya yayin da yake hutawa.

A farkon watan nan Mai girma Bola Tinubu ya dauki hutun makonni biyu da nufin yin nazarin abubuwa da suka shafi kasar.

Mai taimakawa shugaban kasar a kan harkokin siyasa ya kebe da shi, kafin su lula zuwa kasar Faransa ana tsaka da jita-jitar rashin lafiyar Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.