'An Bar wa Allah': Shehu Sani Ya Lissafo Rigingimu 6 da Aka Gaza Magancewa

'An Bar wa Allah': Shehu Sani Ya Lissafo Rigingimu 6 da Aka Gaza Magancewa

  • Sanata Shehu Sani ya ce rikice rikice shida ne a Najeriya da yanzu aka barwa Allah ya magance su yayin da jama'a suka gaza
  • Tsohon sanatan na Kaduna ta tsakiya ya ce rikice-rikicen sun hada da wanda ake yi tsakanin Siminalayi Fubara da Nyesom Wike
  • Sauran rigingimun sun hada da na masarautar Kano da kuma takaddamar NNPC da matatar Dangote da kuma wasu matsaloli uku

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya bayyana manyan rigingimu shida da ke faruwa a Najeriya.

Tsohon sanatan ya ce a yanzu dai an barwa Allah ya magance wadannan rigingimun yayin da al'ummar kasar suka gaza yin katabus.

Kara karanta wannan

Yar’adua, Saraki da sauran gidajen siyasa 10 da suka fi shahara a Najeriya

Sanata Shehu ya yi magana kan rigingimun Najeriya da aka gaza magancewa
Shehu Sani ya lissafo rikice-rikicen Najeriya da aka barwa Allah ya magance. Hoto: @ShehuSani
Asali: Facebook

Sanata Shehu Sani ya bayyana hakan ne a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter) a ranar Juma'a, 11 ga wata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga rigingimu shida da aka barwa Allah ya magance su da kansa:

1. Nyesom Wike vs Gwamna Fubara

Sani ya ce an barwa Allah ya magance rikicin siyasa tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike a jihar Ribas.

2. Rigimar masarautar Kano

Ya ce Allah ne kadai zai iya warware rikicin masarautar Kano tsakanin Mai Martaba Sarkin Kano Muhammad Sanusi II da sarkin da aka tsige, Aminu Ado Bayero.

3. Dauda Lawal vs Bello Matawalle

Sanata Sani ya ce akwai kuma rigimar gwamnan Zamfara, Dauda Lawal da karamin ministan tsaro, Muhammed Bello Matawalle kan rikicin daukar nauyin 'yan bindiga da rashin tsaro a jihar.

Kara karanta wannan

'Ba laifinsa ba ne', Ndume ya fadi nufin Tinubu, ya roki alfarma bayan tsadar fetur

4. Rikicin jam'iyyar Labour (LP)

Rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar Labour Party (LP) sakamakon rigimar shugabanci da batun tsige shugabanta Julius Abure shi ma ya shiga jadawalin Sanata Sani.

5. Takun sakar NNPC da Dangote

Akwai kuma rikicin kamfanin NNPC da Aliko Dangote kan farashin mai da karancin man fetur bayan cire tallafin mai da gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Bola Tinubu ta yi.

6. Rikicin shugabancin PDP

Sanata Sani ya ce an barwa Allah ya magance rikicin cikin gida na jam’iyyar PDP bayan wani bangare ya dakatar da shugaban riko na kwamitin gudanarwa karkashin Umar Damagum.

Duba jadawalin a kasa:

Matsaloli 7 da suka addabi Arewa

A wani labarin, mun ruwaito cewa Sanata Shehu Sani ya ce jihohin Arewa na fama da hare-haren 'yan ta'adda, fadan kabilanci da na addini wanda ya gusar da zaman lafiya a shiyyar.

Shehu Sani ya ce Arewa na fuskantar wasu nau'ikatan rikice-rikice guda bakwai, tare da alakanta kowacce jiha da matsalar da take fama da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.