‘Ba Daidai ba ne’: Malamin Musulunci Ya Sha Suka kan Magana game da Karin Kudin Mai
- Mutane da dama sun caccaki Malamin Musulunci kan bayanansa bayan Gwamnatin Tarayya ta kara kudin mai
- Sheikh Abdallah Usman Gadon Kaya ya yi magana ne kan karin kudin mai inda ya yi addu'ar samun kudin siya ko nawa farashi
- Wannan addu'a ta malamin ba ta yiwa jama'a da dama dadi ba inda suka ce wannan ba ita ce addu'ar da ta dace ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Malamin Musulunci, Sheikh Abdallah Usman Gadon Kaya ya yi magana bayan karin farashin mai.
Sheikh Gadon Kaya ya ce ko nawa gwamnati ta ga dama ta kara farashin suna fatan Allah ya basu kudin siya.
Kudin mai: Malamin Musulunci ya yi magana
Malamin ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da shafin Karatuttukan malaman Musulunci ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Gadon Kaya ya yi addu'ar Allah ya ba mutum kudin da zai sayi komai da ke da tsada a rayuwa.
"Idan za su kai litar man fetur N1m, idan Allah ya baka aiki da sana'a da za ka samu bata yi maka tsada ba."
"Su je su yi ta bunka mata kudi yadda suka ga dama kai kuma ka yi addu'ar Allah ya baka abin da za ka siya."
"Idan rigar mutum daya ta kai N20m, kawai ka yi ta addu'ar Allah a baka miliyan 20 da yawa yadda za ka siya."
- Sheikh Abdallah Gadon Kaya
Martanin wasu mutane kan maganar malamin
Wannnan karatu na Sheikh Gadon Kaya ya jawo cece-kuce inda mutane da dama suke korafi kan addu'ar malamin.
Nasiru Abubakar Wundi:
"Gaskiya wannan magana sam ba dai dai ba ne, N1m fa kace, wannan ya sabawa hankali da tunani."
Musa Ibrahim:
"Wannan surutun banza kawai ya rage a bakinku."
Ak Ibrahim:
"Hakan na nufin idan jifa ya wuce kanka ya fada kan uban kowa kenan, to gaskiya da sake."
Lawal Yusuf:
"Kaji rashin adalci na magana."
N16m: Malami ya ƙaryata karbar kuɗi
Kun ji cewa Sheikh Abdullahi Usman Gadon Kaya ya rufe bakin masu zargin cewa malamai sun samu makudan miliyoyi kwanaki.
Malamai sun nemi zama da jami’an Gwamnatin Tarayya da aka ji labarin yarjejeniyar SAMOA, sai aka juya lamarin.
Asali: Legit.ng