Mutane 16 ‘Yan Gida 1 da Suka Shiga Fagen Siyasa kuma Suka Shahara a Najeriya
Abuja - Akwai wasu mutanen da suka fito daga gida kuma kuma suka rungumi harkar siyasa domin samun mukaman gwamnati.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
A rahoton nan, Legit Hausa ta yi kokarin lalubo ‘yan gida gudan da su ke siyasa kuma har ta kai sun shahara da harkar a Najeriya.
'Yan gida daya tare a harkar siyasa
1. Ahmad Babba-Kaita da Kabir Babba-Kaita
A shekarun baya Kabir Babba-Kaita ya tsaya takara da kaninsa, Ahmad Babba-Kaita domin neman Sanatan jihar Katsina ta Arewa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daily Trust ta ce Ahmad Babba-Kaita ya tashi a hannun yayansa wanda a karshe ya doke shi da APC ta yi galaba a kan jam’iyyar PDP.
2. Orji Uzor Kalu da Mascot Uzor Kalu
Ana shirin zaben 2023 tashar Channels ta ce Mascot Uzor Kalu ya fice daga APC, ya koma APP da niyyar zama gwamna a jihar Abia.
Mascot Uzor Kalu kanin Sanata Orji Uzor Kalu ne wanda kafin zamansa ‘dan majalisar dattawa, ya yi gwamna na shekaru takwas.
3. Rabiu Kwankwaso da Yahaya Kwankwaso
Rabiu Musa Kwankwaso ya shahara a siyasa, ya rike gwamna, ‘dan majalisar wakilai, sanata da kuma minista a lokuta dabam-dabam.
Abin da da yawa ba su sani ba shi ne yana da kani, Yahaya Musa Kwankwaso da ya jagoranci matasan Kwankwasiyya kuma ‘dan siyasa ne.
Yanzu haka Yahaya Musa Kwankwaso ya na rike da mukamin DCoP a gwamnatin jihar Kano.
4. Bala Shagari/Mukhtar Shagari
Marigayi Bala Shagari zai iya shiga cikin ‘yan siyasa, ya wakilci Yabo, Shagari da Tambuwal da za a shirya kundin tsarin mulki a 1988.
Shi kuwa kaninsa, Mukhtar Shagari cikakken ‘dan siyasa ne wanda ya nemi gwamnan Sokoto, kwanaki ya bar PDP zuwa APC mai-ci.
5. David Umahi/Austin Umahi
David Umahi ya yi shekaru takwas a kujerar gwamnan Ebonyi daga baya kuma ya koma Sanata, daga nan ne ya zama ministan ayyuka.
‘Danuwansa, Austin Umahi ‘dan siyasa ne wanda ya rike shugaban jam’iyyar APC kuma har ya so ya yi takarar Sanatan Ebonyi ta Kudu.
6. Isiaka Adeleke/Ademola Adeleke
Marigayi Isiaka Adeleke ya rasu ya na kan kujerar Sanata mai wakiltar yammacin Osun. The Cable ta ce ya cika ya na mai shekaru 62.
Ba a dade ba sai kaninsa ya bi sahunsa, Ademola Adeleke ya zama gwamnan jihar Osun kuma ya gaji sarautarsa ta Asiwajun kasar Ede.
7. Andy Uba/Chris Uba
Sanata Andy Uba likita ne wanda ya fara zama hadimin Olusegun Obasanjo. A 2007 ya zama gwamnan Anambra, ya yi kwanaki 17 ne a ofis.
Kaninsu Chris Uba shi ma ‘dan siyasa ne wanda This Day ta ce ya yi suna da ya kitsa yadda aka tsige Chris Ngige daga kujerar gwamna.
8. Bukola Saraki/Gbemisola Saraki
Bukola Saraki 'dan siyasa ne da ya shahara har ya zama gwamna da sanata. A 2015 ya zama shugaban majalisar dattawan Najeriya.
Yaruwarsa Gbemisola Saraki ta rike kujeru kamar na Ministar sufuri da Sanata.
'Yan siyasar da FCTA ta taso a gaba
Malam Ibrahim Shekarau da Adamu Muazu su na cikin wadanda aka ji labari FCTA ke barazanar karbe filayensu a birnin Abuja
A wadanda aka ba wa'adi akwai tsofaffin gwamnoni kamar Theodore Orji, Rochas Okorocha, Ibikunle Amosun da Tanko Al-Makura.
Asali: Legit.ng