An Samu Mutumin Farko da Aka Gani da Tinubu a Ingila, Ya Fadi Halin da Ake Ciki

An Samu Mutumin Farko da Aka Gani da Tinubu a Ingila, Ya Fadi Halin da Ake Ciki

  • Ibrahim Kabir Masari ya yi zama da Bola Ahmed Tinubu a gidansa da ke Birtaniya yayin da yake hutawa
  • A farkon watan nan Mai girma Bola Tinubu ya dauki hutun makonni biyu da nufin yin nazarin abubuwa
  • Mai taimakawa shugaban kasar a kan harkokin siyasa ya kebe da shi, kafin su lula zuwa kasar Faransa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Ibrahim Kabir Masari ya gagara jurewa, ya hau jirgin sama domin ya yi ido biyu da mai gidansa watau shugaban kasa.

A yammacin Juma’a, 11 ga watan Oktoba 2023, Alhaji Ibrahim Kabir Masari ya sanar da cewa ya hadu da Bola Ahmed Tinubu.

Bola Tinubu a Ingila
Ibrahim Kabir Masari ya hadu da shugaba Bola Tinubu a Ingila Hoto: Ibrahim Kabir Masari
Asali: Facebook

Ibrahim Kabir Masari ya ga Bola Tinubu

Kara karanta wannan

'Ba laifinsa ba ne', Ndume ya fadi nufin Tinubu, ya roki alfarma bayan tsadar fetur

Ibrahim Kabir Masari ya bayyanawa duniya a shafinsa na Facebook cewa ya samu damar yin zama da shugaba Bola Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadimin shugaban a kan harkar siyasa ya sanar da cewa sun yi muhimman zama da ake sa ran sun haifar da da mai ido.

Masari ya ce Tinubu zai wuce Faris

Bayan tattaunawar da suka yi, Ibrahim Masari ya kara da cewa daga nan za su wuce kasar Faransa domin cigaba da magana.

Ba wannan ne karon farko da aka ji Bola Tinubu ya ziyarci Faris, babban birnin Faransa ba, ya saba yin ganawar siyasa a can.

Jim kadan bayan ya wallafa haka a shafinsa na X da kimanin karfe 3:00 na yamma, mutane sun maidawa ‘dan siyasar amsa.

Jita-jita game da halin da Tinubu yake ciki

Ziyarar ta zo ne a lokacin da Legit Hausa ta samu labari wasu sun fara yada jita-jita cewa shugaban kasa Tinubu bai da lafiya.

Kara karanta wannan

'A fita zanga zanga,' Yadda aka yi rubdugu ga Tinubu kan tashin kudin fetur

Babu mamaki wannan ziyara ta rufe bakin masu kirawa shugaba Tinubu rashin lafiya.

Ana sa ran cewa ba da dadewa ba, Mai girma Bola Tinubu zai dawo Abuja domin hutun da ya dauka ya kusa zuwa karshe.

Legit Hausa ta lura tun da ya bar Najeriya zuwa Birtaniya, kusan wannan ne karon farko da aka gan shi ya zauna da wani.

An ba Bola Tinubu shawara

A yau $1 ta kusa kai N2000, ana da labari Kalu Aja ya nemi a karya Dala domin a shigo da abinci daga waje domin a samu sauki.

Idan ‘yan kasuwa su ka samu $1 a N200, masanin tattalin arzikin ya ce abinci zai sauko a yanzu da buhun shinkafa ya kai N100, 000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng