Matar Shugaba Tinubu Ta Nuna Halin Girma, Ta yi Kyautar Kudi N1bn

Matar Shugaba Tinubu Ta Nuna Halin Girma, Ta yi Kyautar Kudi N1bn

  • Matar shugaban kasa, Oluremi Bola Tinubu ta kai ziyara jami'ar Obafemi Awolowo (OAU) ta da yi karatu shekarun da suka wuce
  • Oluremi Bola Tinubu ta nuna rashin jin dadi kan yadda ta ga jami'ar musamman wajen rashin tsaftar muhalli da gyare-gyare
  • Biyo bayan haka, matar shugaban kasar ta yi kyautar kuɗi har Naira biliyan daya ga jami'ar domin cigaba da kula da makarantar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Matar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ta kaddamar da titi a jami'ar Obafemi Awolowo.

Bayan kaddamar da titin, Oluremi Tinubu ta zagaya makarantar inda ta koka kan yadda lamura suke a halin yanzu.

Kara karanta wannan

'A fita zanga zanga,' Yadda aka yi rubdugu ga Tinubu kan tashin kudin fetur

Matar Tinubu
Matar Tinubu ta yi kyautar N1bn. Hoto: @SenRemiTinubu
Asali: UGC

The Guardian ta wallafa cewa Oluremi Tinubu ta yi kyautar kuɗi mai yawa a makarantar domin farfaɗo da gine gine da tsaftar muhalli.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matar Tinubu, Remi ta yi kyautar N1bn

Matar shugaban kasa, Oluremi Bola Tinubu ta yi kyautar N1bn ga jami'ar Obafemi Awolowo a lokacin da ta kai ziyara.

Oluremi Tinubu ta je ziyara OAU ne domin ƙaddamar da titi mai nisan kilomita 2.7 da aka sanyawa wuta mai amfani da hasken rana.

Uwargidar Tinubu ta koka da ta ga jami'ar OAU

Remi Tinubu ta ce a lokacin da suke makarantar shekaru 41 da suka wuce ana tsaftace jami'ar sosai amma ba ta ji dadin abin da ta gani ba.

Ta ce ya kamata a dawo da tsaftar muhalli kamar yadda ake a shekarun baya wanda su da kansu suke share filin makarantar.

Remi Tinubu ta yabi Ooni na Ife

Kara karanta wannan

"Ba laifin mijina ba ne": Uwargidan Tinubu ta fadi lokacin da talaka zai samu sauki

Matar shugaban kasa Bola Tinubu ta yi godiya ga Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi kan yadda yake kula da jami'ar.

Leadership ta wallafa cewa Remi Tinubu ta taya Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi murnar cika shekaru 50 da haihuwa da ya yi.

Matar Tinubu ta raba kudi a Zamfara

A wani rahoton, kun ji cewa Oluremi Tinubu ta raba miliyoyin kudi ga mata a jihar Zamfara domin bunkasa ƙananan sana'o'i.

An ruwaito cewa mata 1,000 ne suka samu kyautar tallafin a wannan karon yayin da matar shugaban kasar ta samu wakilci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng