"Ba 13 ba ne:" Gwamnatin Borno Ta Fadi Adadin Tubabbun Yan Boko Haram da Su ka Gudu
- Gwamnatin Borno ta bayyana ainihin adadin tubabbun yan Boko Haram da su ka tsere daga wurin da ake ba su horo
- Labarin da ya fito tun da fari ya nuna tubabbun mayakan Boko Haram akalla 13 ne su ka tsere daga inda aka ajiye su
- Rahotannin sun ci gaba da cewa mayakan sun kuma kwashi wasu makamai, amma gwamnati ta musanta haka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno - Gwamnatin Borno ta yi gyara kan adadin tubabbun yan Boko Haram da su ka tsere daga wurin da ake ba basu horo.
Rahotannin da aka samu da fari sun bayyana cewa wasu mutum 13 daga cikin tubabbun mayakan Boko Haram ne su ka gudu da makaman sojoji.
Jaridar The Cable ta wallafa cewa Kwamishinan yada labarai da tsaron cikin gida, Usman Tar ya bayyana cewa wadanda su ka gudu ba su kai 13 ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan Boko Haram nawa ne suka tsere?
Jaridar Zagazola ta tattaro cewa gwamnatin Babagana Zulum ta jihar Borno ta ce tubabbun mayakan Boko Haram shida ne su ka gudu.
Gwamnatin ta kara da cewa mayakan da ake ba su horo bayan sun tuba daga ayyukan ta'addancin ba su dauki makamai ba kamar yadda aka ruwaito a baya.
Ana neman mayakan Boko Haram
Kwamishinan yada labarai da tsaron cikin gida a Borno, Usman Tar ya ce akwai bayanan tubabbun yan ta'adda shida da su ka gudu daga inda ake kebe su.
"Sun gudu ba tare da daukar makamai ba kuma yanzu haka ana nemansu ruwa a jallo. Bayanan da aka fitar da farko na cewa sun gudu da makaman gwamnati ba gaskiya ba ne,"
- Kwamishinan jihar Borno
Tubabbun mayakan Boko Haram sun tsere
A baya kun ji cewa wasu tubabbun dakarun Boko Haram da ke karbar horo daga gwamnatin kasar nan saboda tuba daga ayyukan ta'addanci sun tsere daga hannun gwamnati.
Sama da tubabbun yan Boko Haram 2,000 ne ke karbar horo, inda daga bisani a kan dauke su wajen taimaka wa sojojin da ke yaki da ta'addanci wajen shiga a Borno.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng